An bai wa kasurgumin dan bindiga sarautar gargajiya a Zamfara

Nadin sarautar dai ya jawo cece-kuce

An bai wa kasurgumin dan bindiga sarautar gargajiya a Zamfara

Dan bindiga Ado Aleiro

Masarautar ’Yandoton Daji da ke jihar Zamfara, ta nada kasurgumin dan bindigar nan da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro, sarautar Sarkin Fulanin ’Yandoto ranar Asabar.

An gudanar da bikin nadin ne ’yan sa’o’i bayan masarautar ta sanar da fasa nadin tun da farko.

Sarkin na ’Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa tun da farko ya yi shirn nada Aleiron sarautar ranar Asabar, amma ya dage bikin ’yan sa’o’i sakamakon umarnin gwamnatin jihar, kamar yadda bayanan da Aminiya ta tattara suka nuna.

Batun nadin nasa ya biyo bayan irin rawar da masarautar ta ce ya taka a ’yan watannin baya tsakanin masarautar da ’yan bindigar da suka addabi Karamar Hukumar Tsafe da ke jihar ta Zamfara.

Aminiya ta gano cewa gwamnatin jihar dai tun da farko ta ba da umarnin dakatar da nadin ne saboda gudun cece-kucen da hakan zai iya jawowa idan labarin ya fita.

Bikin nadin sarautar dai, wanda aka yi a fadar masarautar ta ’Yandoton Daji, ya sami halartar Shugaban Karamar Hukumar Tsafe da kuma Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, DIG Mamman Tsafe (mai ritaya).

A cewar wata majiya, “Bikin ya kuma sami halartar shugabannin ’yan bindiga da dama tare da dakarunsu da suka je a kan babura.

“Sun bi ta hanyar Gusau zuwa Funtuwa, inda suka yada zango a Gidan Dawa, inda mutanen garin suka ba su katan-katan na lemukan sha a matsayin gudunmawa,” inji majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta.

“Amma babu tabbaci ko shi Aleron ya yi jawabi yayain bikin nadin, amma daya daga cikin na hannun damansu wanda ya yi jawabi ya koka da yadda ya ce mutane na kiransu da ’yan ta’adda,” inji mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Sufyan.

“Mu ba ’yan fashi ba ne kuma ba ’yan ta’adda ba, amma muddin ana so zaman lafiya ya dawo, dole gwamnatin jiha ta ta tarayya su samar mana mu makiyaya da filayen kiwo da makarantu da asibitoci,” kamar yadda aka ambato shi yana cewa.

A lokacin wani zaman sulhu da ya wargaje daga bisani a shekara ta 2019 tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da ’yan bindigar, wakilan gwamnati sun zauna da Aleiro a garin Munhaye da ke da nisa kilomita 15 a kan hanyar Gusau zuwa Funtuwa.

A lokacin dai ya yi alkawarin ajiye makamansa, amma daga bisani ya sake kai wasu munanan hare-hare Kananan Hukumomin Tsafe da Faskari da Kankara da ke jihohin Zamfara da Katsina.

Jim kadan da yin haka ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta sanya la’adar Naira miliyan biyar ga duk wanda ya kawo mata shi.

Tun daga lokacin ne ya yi ta kitsa hare-hare a yankunan Kananan Hukumomin da ke Tsafe da kuma Faskari a jihohin biyu.

Ayyukan ’yan bindiga dai sun yi matukar illata yankin Arewa maso Yamma, inda suka yi sanadin kashe mutane da dama, aka sace wasu sannan wasu miliyoyi kuma suka rasa muhallansu.