An bai wa marayu 1000 gurbin karo ilimi a Gombe

Wata kungiya mai kula da jin dadin marayu da marasa galihu a Jihar Gombe mai suna Welfare of Orphans and Destitute ta bai wa marayu kimanin guda 1000 tallafin karo ilimi.Da yake jawabi a lokacin ba da tallafin Shugaban kungiyar Da’a wa da Kula da Jin Dadin Marayu Ustaz Muhammad Lawal, cewa ya yi ba […]

An bai wa marayu 1000 gurbin karo ilimi a Gombe
An bai wa marayu 1000 gurbin karo ilimi a Gombe

Wata kungiya mai kula da jin dadin marayu da marasa galihu a Jihar Gombe mai suna Welfare of Orphans and Destitute ta bai wa marayu kimanin guda 1000 tallafin karo ilimi.
Da yake jawabi a lokacin ba da tallafin Shugaban kungiyar Da’a wa da Kula da Jin Dadin Marayu Ustaz Muhammad Lawal, cewa ya yi ba da wannan tallafin karatu da kayayyakin abinci da kula da lafiyar marayun abu ne da ya dace.
Ustaz Muhammad Lawal, ya bayyana cewa Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya samar wa wani da yake da bukata tallafi sakamakonsa gidan aljanna a ranar gobe.
Shugaban ya yaba da irin wannan kyakkyawar aniyya ta kungiyar sannan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da hakan domin zai sa marayun su ji kamar su ba marayu ba ne.
A nasa jawabin daya daga cikin iyayen kungiyar Alhaji Umaru Bello, wanda ya yaba da yadda aka shirya wannan taro don bai wa marayu tallafin ya yi addu’ar dorewar wannan shiri.
Suma a jawabansu mabanbanta kansilan unguwar Jeka da Fari a fadar jihar  Babayo Haruna da wakilin dan majalisar jihar mai wakiltar Gombe ta arewa Alhaji Mohammed Ahmed Bello, wanda  Garba Darazawa ya wakilta alkawari suka yi na ci gaba da tallafawa kungiyar.
Da yake jawabi tun farko shugaban kungiyar Malam Yakubu Sani,  cewa ya yi an kafa wannan kungiyar ce shekaru 18 da suka wuce, da nufin tallafa wa marayu da yara marasa galihu ta hanyar samar musu da abinci da sutura da tallafin karo karatu da kula da lafiyar su da makamantan haka.
Akarshe ya gode wa al’umma na irin tallafin da suka bayar sai ya roke su da su ci gaba da tallafa wa kungiyar.