An bai wa mata a Saudiyya ’yancin takara a majalisar kananan hukumomi
Ministan Kula da Birane da yankunan karkara mna Saudiyya, Yarima Mansour bin Miteb, ya bayar da sanarwar izinin gwamnati ga matan kasar na shiga takara da yakin neman zabe.“Mata na da ’yancin yin takarar zabe tamkar maza, ba tare da an nuna musu bambanci ba,” inji shi. Kuma matan Saudiyya suna da ’yancin yakin neman […]

Ministan Kula da Birane da yankunan karkara mna Saudiyya, Yarima Mansour bin Miteb, ya bayar da sanarwar izinin gwamnati ga matan kasar na shiga takara da yakin neman zabe.
“Mata na da ’yancin yin takarar zabe tamkar maza, ba tare da an nuna musu bambanci ba,” inji shi. Kuma matan Saudiyya suna da ’yancin yakin neman zabe kamar maza, kamar yadda aka ruwaito a cikin sanarwar.
Mata masu sa’ido an zabo su daga kungiyoyin al’umma, don kula da halin da mata za su kasance, tare da wakilansu da masu akda kuri’u.
Ya ce kowace ’yar takara za ta zabi wakilinta na rumfar zabe, namiji daya, mace daya, wadanda za su kasance a rumfunan zabe.
Ministan ya ce wannan tsarin an tsara ne bisa ka’idojin shari’ar Musulunci, da kuma tsare-tsaren kasashen duniya na rashin nuna wariya ga mata. Za a bai wa matan katin shaidar dan kasa, don su samu damar yin takara, ko su kada kuri’a.
Shi ma Sarki Abdullah, mai hidima ga masallatai masu alfarma, ya bayar da umarnin kyale mata su zama ’yan majalisa a kananan hukumomi. Wannan sanarwa ta sanya wa mata farin ciki. Fatima Mossalli, daya daga cikin ’yan kungiyar Baladi mai fafutikar hakkokin mata, ta nuna farin cikinta kan yadda suka karbi wannan sako.
Suhaila Zain Al-Abideen, wata mai fafutikar hakkin yara da mata, ta ce lokaci ya yi da al’umamr Sazudiyya za su fara amincewa da shugabancin mata. “Lokaci ya yi da za mu fara fadakarwa kan muhimmancin rike mukaman mata a majalisun kananan hukomi.” Injita.
Ta kuma bukaci masu hannu da shuni su taimaka wa mata da kudin yakin neman zabe. “Mutane da dama ba su da kudi, don haka akwai bukatar tallafin ’yan kasuwa, su taimaka wa ’yan uwansu mata,” a cewarta.