An bai wa Newcastle damar dauko aron ‘yan wasa daga Saudiyya
An kammala cinikin Newcastle a kan Fam miliyan 30 a watan Oktoban 2021.
Za a bar Newcastle United ta rika daukar aron ’yan wasa daga gasar Saudiyya a watan Janairu, bayan da aka kada kuri’a kan batun.
Tun farko kungiyoyin gasar Firmiya ne suka ki amincewa da tsarin, abin da ya kai da dakatar da batun na wani lokaci.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 99, sun kuɓutar da mutum 139 a mako guda
- Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi
Masu buga Firmiya 13 ne suka kada kuri’ar kin amincewa da barin wadda ta mallaki kungiya a gasar ta dauki aron ’yan wasa daga kasarta.
Ke nan zaben ya gaza da kuri’a daya, hakan na nufin Newcastle United za ta iya dauko aron ’yan wasa daga babbar gasar kwallo ta Saudiyya, wato za ta iya dauko aron dan kwallo daga kungiyar da masu hannun jari daga Saudiyya suka mallaka.
An kammala cinikin Newcastle a kan Fam miliyan 30 a watan Oktoban 2021, wadda ake cewa za ta dauki aron tsohon dan kwallon Wolverhampton, Ruben Neves daga Al-Hilal.
Tun farko an dakatar da bukatar hakan na dan lokaci har zuwa lokacin da za a cim ma matsaya kafin a bude kasuwar sayar da ’yan kwallo ta Nahiyar Turai.
Amincewar tana nufin sai dai a dauko aron dan wasa ba wai a bayar da aronsa daga Newcastle zuwa gasar Saudiyya ba.
Masu zuba jari daga Saudiyya suna da kaso 80 cikin 100 a Newcastle, wadda ta mallaki manyan kungiyoyi hudu a Saudiyya a watan Yuni.
Kungiyoyin sun hada da Al-Nassr da Al-Hilal da Al-Ahli da kuma Al-Ittihad.