An baiwa mata rancen naira miliyan 100 a Sokoto
Daya daga cikin ‘yan gudun hijira Amina a sansanin ‘yan gudun hijira na Gandi dake karamar hukumar Raba jihar Sakkwato ta yi murnar sanarwar dake cewa za a baiwa mata ‘yan gudun hijira 1,000 naira miliyan 100 rance. Amina ‘yar shekara 45 wanda take zaune a sansanin ‘yan gudun hijira ta bayyana muhimmancin kudin da […]
Daya daga cikin ‘yan gudun hijira Amina a sansanin ‘yan gudun hijira na Gandi dake karamar hukumar Raba jihar Sakkwato ta yi murnar sanarwar dake cewa za a baiwa mata ‘yan gudun hijira 1,000 naira miliyan 100 rance.
Amina ‘yar shekara 45 wanda take zaune a sansanin ‘yan gudun hijira ta bayyana muhimmancin kudin da za a basu don su dogara dan kansu. Ta kara da cewa, ta rasa maigidanta da duk wasu kadarorinta sanadiyyar harin barayi a Tabanni da sauran kauyukan Raba, ta dai dogara ne da tallafin gwamnati da ake basu a sansanin Gandi.
Adadin ‘yan gudun hijira 5,127 ne daga kauyukan Tabanni da Alikiru da Kwasa da Warwanna da Gidan Kare da Ruwan Tsamiya da Ilulu da Dutsi da Tafkin Kwasa, akwai mata 1,770 da kuma maza 1,227 sai ‘yan mata 1,197 da kuma yara maza 933.