An bankaɗo inda ake sauya wa shinkafar tallafi buhu a Kano
Hukumar ta gano rumbun wanda ake sauya wa shinkafar tallafi buhu ake sayarwa a kasuwanni.
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta bankaɗo wani rumbun ajiya da ake amfani da shi wajen sauya buhun shinkafar tallafi ta Gwamnatin Tarayya, don sayarwa a kasuwa.
An gano buhun shinkafar da aka rubuta “Bana sayarwa ba ne”.
- Tinubu ya yaba wa NNPCL kan farfaɗo da matatar mai ta Fatakwal
- An rufe bakuna 3 kan rashin biyan haraji a Kaduna
Buhun na ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda aka raba lokacin rabon tallafin watan Ramadan na bara.
An ajiye su a wani rumbun ajiya da ke kusa da Farin Masallaci a kan titin Hotoro Ring Road, inda manyan motoci guda 28 ɗauke da buhun shinkafar.
Yayin samamen, Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce, “Muna binciken rahotannin da ke cewa wasu suna amfani da tallafin Gwamnati wajen sauya buhun shinkafa domin sayarwa.
“Wannan aiki ƙarara cin hanci ne, musamman a wannan lokaci na wahala da muke ciki a ƙasa.”
Ya ƙara da cewa, “Mun kama su yayin da suke tsaka da aikin canja buhun shinkafar.
“Zuwa yanzu, mun kama mutum ɗaya, kuma za mu ci gaba da bincike domin gano waɗanda suke da hannu a lamarin. Za mu ɗauki matakan doka domin daƙile irin waɗannan ayyuka.”
A cewar Rimingado, kowace daga cikin motocin 28, tana ɗauke da kimanin buhun 600 na shinkafa, kuma kowane buhu kuɗinsa ya kai Naira 82,000.
Jimlar kuɗin shinkafar ya kai kimanin Naira biliyan 1.3.