An bankaɗo ma’aikatan bogi 427 a Anambra

Akwai ma’aikatan jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka da Kwalejin Ilimi ta Nwafor Orizu da ke Nsugbe.

An bankaɗo ma’aikatan bogi 427 a Anambra

Hukumar Ma’aikatan Ƙananan hukumomin Jihar Anambra ta gano sama da ma’aikatan bogi 427 da ke karɓar albashi daga gwamnati.

Daga cikin ma’aikatan bogin akwai ma’aikatan hukumar 59 da suka mutu da daɗewa, da wasu 40 da suka yi ritaya kuma har yanzu suna kan karɓar albashin hukumar.  Yayin da wasu kimanin 11 ke zaune a ƙasashen waje.

Shugaban Hukumar, Vin Ezeaka ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Awka, babban birnin Jihar Anambra.

Ya ce, an gano hakan ne a yayin da aka yi wani binciken ma’aikatan da aka ƙaddamar domin tsaftace tsarin ƙananan hukumomin jihar.

Ya ce an gano wani abin ban mamaki na sama da ma’aikata 427 da ke cikin tsarin albashin ƙananan hukumomi ba tare da sun kasance ma’aikata ba.

Ezeaka ya ce, wasu daga cikin waɗanda aka gano akwai ma’aikatan Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka da Kwalejin Ilimi ta Nwafor Orizu, a Nsugbe.

“Mun gano ma’aikata 59 da suka mutu waɗanda har yanzu suke karɓar albashi, 40 da suka yi ritaya su ma suna karɓar albashi.

“Bayan haka, mun gano ma’aikata 222 a cikin takardar biyan albashin da babu wanda zai iya tantance ma’aikata a cikin ƙananan hukumomin 21.

“Sannan kuma akwai da yawa daga cikinsu da ke zaune a ƙasashen waje amma har yanzu suna karɓar albashi.

“Don haka muka rubuta ƙorafi zuwa ga masu harkar asusun haɗaka, JAC don cire su daga tsarin albashi.

“Wasu daga cikinsu sun yi ritaya sun zo ne don son rai, amma mun ƙi amincewa da buƙatarsu, saboda ba zamu yaudari gwamnati ba, kuma kuna son yin ritaya.

“Za mu gama bincikenmu kuma waɗanda muka kama da wannan rashin gaskiya za su fuskanci fushin doka kamar yadda dokar ma’aikata ta tanadar.”

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara