An banka wa gidan Sarkin Yakawada wuta kan kisan wata yarinya

An kone gidan Sarkin Yakawada, Alhaji Rilwanu Sama’ila da ke karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna a sakomakon zarginsa da al’ummar garin suka yi da kisan wata yarinya da aka tsinci gawarta a cikin wani kango da ke kusa da gidan shakatawarsa.Tsintar wannan gawar ta Hadiza Musa ’yar shekara tara ya tayar da hankalin al’ummar […]

An banka wa gidan Sarkin Yakawada wuta kan kisan wata yarinya
An banka wa gidan Sarkin Yakawada wuta kan kisan wata yarinya

An kone gidan Sarkin Yakawada, Alhaji Rilwanu Sama’ila da ke karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna a sakomakon zarginsa da al’ummar garin suka yi da kisan wata yarinya da aka tsinci gawarta a cikin wani kango da ke kusa da gidan shakatawarsa.
Tsintar wannan gawar ta Hadiza Musa ’yar shekara tara ya tayar da hankalin al’ummar wannan gari, musamman da yake wannan ba shi ne karo na farko da aka tsinci irin wannan gawa a kusa da gidan mai garin ba, wanda sau da yawa akan samu an cire wani sashi na jikin gawarwakin da ake tsinta.Wannan tasa mutanen garin suka shirya zanga-zanga inda suka dumfari gidan shakatawar sarkin suka banka masa wuta.
A yayin da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Sarkin sai ya ce, “ni yanzu ba zan iya ce maka komai ba saboda ina cikin tashin hankali”. Don haka ya bayar da izini ga wakilin namu don ya shiga gidan ya gane wa idanunsa abin day a faru, inda ya ga yadda makarraban sarki ke kokarin kashe wutar da aka kunna wa gidan shakatsawar sarkin.
Wani wakilin sarki mai suna Sadik Sani, Turakin Sarkin Yakawada, ya bayyana wa Aminiya cewa, dawowarsa daga asibiti wurin aikinsa ke nan sai aka zo masa da labarin cewa an tsinci gawar wata yarinya a inda suke karatun islamiyya. Sai ya buga wa sarki waya, inda sarki ya gaya masa cewa shi yana garin Giwa tun safe. ‘’Daga nan sarki sai ya yi maza ya dawo ya kira babban jami’in ‘yan sanda (DPO), bayan ‘yan sanda sun iso suka duba, sai kawai matasa suka ce ai ga ma jini nan a wajen gidan sarki, alhali kuwa karya ne babu wani jini. Ai fa daga nan sai suka alakanta kisan yarinyar da cewa mu muka kashe ta, sai suka hau mu da jifa, suka ce sai sun kashe mu, suka nufo gidan sarki inda suka kunna wa gidan wuta, ni kuma suka farfasa gilashin gidana, suka ce za su dawo su kona gidan.’’
 Da Aminiya ta tamabaye shi ko irin haka ya taba faruwa? Sai Turakin Yakawada ya ce, ‘’ei haka ya taba faruwa, domin a shekarar da ta wuce haka aka kashe wata yarinya ita ma aka ce an cire wani abu a jinkinta, amma ni ban gani ba don ba na nan, ina rokon Allah Ya tona asirin mai aikata mana wannan mugun alkaba’i.’’
Wakilinmu ya ziyarci gidan iyayen yarinyar da aka tsinci gawarta inda ya zanta da mahaifinta Musa Abdullahi, wanda ya bayyana cewa, ‘’bayan yariyar ta dawo daga makaranta ta bukaci ta ci abinci, sai na ce ta je ta kira mai abinci a saya mata saboda babarta ba ta nan ta tafi unguwa. Sai ta dauki taya tana garawa don ta kirawo mai abincin, daga nan na ji shiru, sai na tambaya na ce ina mamata? Na ji shiru! Har na gaji na tafi bakin kasuwa, ina zaune sai na ji labarin an tsinci gawar wata yarinya a kusa da gidanmu kuma an kwakule mata idanu, sai na taso don in ga ko wace ce, ina isowa sai na ga tayarta da takalminta a tsakar gidan. Daga nan na tabbatar da cewa Hadiza ce, sai tausayi ya kama ni na dawo da baya, sai samari suka dauko ta suka kawo min ita.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’jami’an tsaro sun yi kokarin daukar gawar don a kai ta asibiti a bincika amma na ce, a bar min ‘yata, ni na bar wa Allah, na yi imani da cewa wannan kaddara ce daga Allah.’’
Ita kuwa mahaifiyar yarinya, watau Hadiza Musa cewa ta yi, dawowarta ke da wuya daga unguwa sai aka gaya mata cewa an yanka ‘yarta, ta fara bayani ke nan sai ta fashe da kuka tana cewa, ‘’Allah ka yi mana sakayya.’’
A hirarsa da manema labarai jim kadan bayan faruwar wannan al’ammarin, Shugaban karamar Hukumar Giwa Alhaji Tsoho Yakawada cewa ya yi, abu na farko da suka fara yi shi ne tura jami’an tsaro wajen domin su kwantar da fitinar da ta taso.
A kan rade-radin da ake yi na cewa wannan ba shi ne karo na farko da faruwar wannan al’amarin ba, sai ya ce, ‘’irin haka ya taba faruwa, amma ita ma ba za a ce ga abin da ya kashe ta ba, domin sai bayan kwana bakwai aka tsinci gawarta a gona,  ganin cewa a wajen farjinta akwai rauni sai muke zargin cewa wani ne ya yi amfani da ita ya kashe ta ya jefar, ita ma wannan idan Allah Ya yarda mun sanya jami’an asibiti su duba ta kuma duk sakamakon da aka samu zamu  fada wa mutane.’’
Dangane da wannan al’amarin kuwa, sai ya ce, ‘’shi ma zargi ne mara tushe, babban abin da ya kamata a yi shi ne a dinga addu’a har Allah Ya tona asirin wadanda suke yin wannan aika-aika.’’
Da wakilinmu ya tuntubi kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna Mista Olufemi Adenike ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, kuma ya ce suna ci gaba da bincike don gano wadanan bata-garin.