An bankado ma’aikatan bogi masu yawa a Jihar Bauchi – Kwamared Sabo
Kwamared Sabo Muhammed tsohon Daraktan Watsa Labarai na tsohuwar Jam’iyyar ANPP ta kasa a yanzu Babban Mai tallafa wa Gwamnan Jihar Bauchi kan Harkokin Watsa Labarai da Hulda da Jama’a a tattaunawarsa da wakilinmu a Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin jihar ke ci gaba da aikin tantance ma’aikata, inda ya ce sun […]
Kwamared Sabo Muhammed tsohon Daraktan Watsa Labarai na tsohuwar Jam’iyyar ANPP ta kasa a yanzu Babban Mai tallafa wa Gwamnan Jihar Bauchi kan Harkokin Watsa Labarai da Hulda da Jama’a a tattaunawarsa da wakilinmu a Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin jihar ke ci gaba da aikin tantance ma’aikata, inda ya ce sun bankado ma’aikatan bogi masu yawa a jihar:
Mene ne dalilin da ya sa kuka fara aikin tantance ma’aikatan Jihar Bauchi?
Dukkan godiya ya tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Abin da ya sa gwamnati Jihar Bauchi a karkashin Gwamna Mohammed Abubakar ta fara aikin tantance ma’aikata shi ne akwai rade-radin da aka samu cewa akwai mutane masu dimbin yawa da suke karbar albashi duk wata amma a matsayin malamai amma duk bogi ne babu su babu alamarsu. Don haka gwamnatin ta ce ya zamo wajibi a tantance duk wani ma’aikacin da yake daukar albashi a Jihar Bauchi. Kuma akwai wasu makarantu da gwamnati take ba su kudi duk wata amma kuma da aka gudanar da bincike sai aka gano babu makarantun kwata-kwata.
Na uku akwai dimbin koke-koke na daukar malamai wadanda ba kwararru ba, don haka Gwamna ya ba da umarni a gudanar da bincike na gaskiya a ba shi rahoto a hukumance domin ya bayyana wa al’ummar jihar gaskiyar abin da yake faruwa. Daga bisani sai aka fara aikin gwaji a kananan hukumomi hudu daga cikin 20 da muke da su a jihar. A kananan hukumomin hudu da aka yi aikin gwaji an gano sama da malamai 80 wadanda aka dauke su aiki da takardun bogi wadanda ba su ne suka yi karatun ba, sun aro ne daga wajen wadansu. Sannan Babban Bankin Najeriya ya ba da umarni ga duk wanda yake da asusun ajiya ya zo a tantance shi tare da daukar hotonsa a bashi lambar da ake kira BbN. Sakamakon haka an gano ma’aikatan bogi sama da dubu 22.
Muna da ’yan fansho a jiha da kananan hukumomi sama da dubu 10, kuma ma’aikatan Jihar Bauchi dukkansu mutum dubu 91 ne har da ’yan fansho. Sakamakon aikin tantancewar, gwamnatin Jihar Bauchi ta samu rarar sama da Naira miliyan 91 don haka gwamnati ta ci gaba da aikin tantancewa domin watakila za ta sake samun wasu rarar kudi masu dimbin yawa da za a ci gaba da ayyuka ga jama’a da su.
Akwai wasu daga cikin mutanen Jihar Bauchi da ba sa goyon bayan a ci gaba da aikin tantance ma’aikata da malaman makaranta, dalili shi ne watakila asirinsu zai tono. Gwamna Mohammed Abubakar ya yi rantsuwa da kur’ani cewa zai yi adalci a lokacin mulkinsa kuma masu hankali da ilimi da sanin ya kamata sun gamsu da haka. Gwamnatin Jihar Bauchi tana da manufofi masu kyau na inganta rayuwar al’umma domin talakawa ne suka zabi canji kuma Allah Ya tabbatar da haka. Gwamna Mohammed Abubakar ya kudiri aniyyar gyara tsarin aikin gwamnati da yadda ake gudanar da harkokin mulki. Duk ma’aikacin da ake hada baki da shi domin cutar jihar ko yi mata zakon kasa zai dandana kudarsa a wannan karon domin gwamnatin APC ta sha bamban da ta PDP wadda ta lalata kusan komai a jihar. Kwamitin Malam Salihu Lukman Abubakar ya gano yaro dan shekara takwas a duniya a karamar Hukumar Giyade yana daukar albashi tun yana ciki kuma gwamnati za ta hukunta wanda ya sanya shi. Akwai wasu kudi da aka samu a boye sama da Naira biliyan takwas, Gwamna zai bayani dalla-dalla ga al’umma ta kafafen watsa labarai nan gaba.
Akwai korafin cewa ba komai a asusun jihar lokacin da kuka karbi mulki mene ne gaskiyar magana?
Lokacin da Barista Mohammed Abubabakar ya karbi ragamar gwamnatin Jihar Bauchi a talauce muka samu asusun gwamnati. Don haka ya toshe dukkan hanyoyin da ake cuwa-cuwa da kudin al’umma ya fito da sababbin dabaru don inganta rayuwar mata da matasa kuma yanzu haka kwalliya ta fara biyan kudin sabulu. Mun biya bashin albashin ma’aikata na wata hudu da aka cinye a lokacin mulkin Gwamna Yuguda wadda ta yi abin da ta ga dama da dukiyar al’umma. Nan da kwanaki kadan masu zuwa gwamnatin za ta daukin sababbin ma’aikata matasa wadanda suka kammala karatu amma suke zaman kashe wando.
Mene ne sakonka ga malaman makarantun firamare da al’umar Jihra Bauchi?
Babban sakona ga malaman makarantun firamare na Jihar Bauchi da ma ’yan siyasa baki daya shi ne Barista Abubakar na sane da halin da mutane suke ciki, kuma abin da ya sa a gaba yanzu shi ne cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfe. Muna fata a cigaba da addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da sauran masu rike da mukaman siyasa. Wadanda suke neman zagon kasa ga wannan gwamnati bukatarsu ba za ta biya ba domin talakawa ne suka zabi canji kuma tabbas an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali sai dai abubuwan da ba a rasawa nan da can. Sakona ga al’ummar Jihar Bauchi shi ne a ci gaba da fatar alheri ga Barista Abubakar wanda ya karbi ragamar gwamnati a lokacin da suke cikin mawuyacin hali sakamakon yadda tsohuwar gwamnati ta lalata komai. Muna fata nan da lokaci kadan kowa zai dara. Domin manufar gwamnatinmu ita ce inganta rayuwar al’umma ta hanyar cika alkawuran da muka dauka na kawar da cuwa-cuwa da babakere da kudin al’umma.