An bankado shirin fafutikar kafa kasar Biyafara a jihohin Yamma

kungiyar Yarbawa zalla ta OPC, ta gano alamar zakudawa da fafutikar kafa kasar Biyafara daga sashin Kudu maso Gabas zuwa Kudu maso Yamma, wanda ta ce ba za ta sabu ba. Alamar hakan inji ta shi ne, Bikin Ranar Ibo ta Duniya na bana da aka shirya a ranar Asabar a wani sashi na Kudu […]

An bankado shirin fafutikar kafa kasar Biyafara a jihohin Yamma
An bankado shirin fafutikar kafa kasar Biyafara a jihohin Yamma

kungiyar Yarbawa zalla ta OPC, ta gano alamar zakudawa da fafutikar kafa kasar Biyafara daga sashin Kudu maso Gabas zuwa Kudu maso Yamma, wanda ta ce ba za ta sabu ba. Alamar hakan inji ta shi ne, Bikin Ranar Ibo ta Duniya na bana da aka shirya a ranar Asabar a wani sashi na Kudu maso Yamma, inda kungiyar ta ce barazana ce ga tsaro saboda yiwuwar yin amfani da wannan dama wajen matsa wa kabilun Ibo masu fafutikar kafa kasar Biyafara daga Kudu maso Gabas zuwa Kudu maso Yamma.
kungiyar ta fadi haka ne cikin takardar sanarwa dauke da sanya hannun Kwamared Akinpelu Adesina da aka raba ga ’yan jarida a Ibadan. kungiyar ta nuna damuwa a kan al’amarin kuma ta roki jami’an tsaro su sanya ido wajen daukar tsauraran matakai domin samar da zama lafiya a sashin Kudu maso Yamma da kasa baki daya.
Shi kuwa Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudancin Najeriya, kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya umarci Sarakunan Hausawa da ke zaune a Kudu maso Gabas su kwantar da hankalin mutanensu game da zanga-zangar kafa kasar Biyafara da wasu tsiararrun  ’yan kabilar Ibo suke yi, inda suka fara da takurawa ’yan Arewa mazauna sashin. Haka kuma, ya roki jama’ar Arewa su kyale mahukunta su yi aikinsu na tsaron lafiyar kasa ba tare da mayar da martani ga wadannan mutane ba.
Bayanin haka yana kunshe ne cikin takardar sanarwa da ta fito daga fadar Sarkin Sasan, inda ya ce: “A matsayinmu na shugabannin al’umma a wannan sashi na kasa, wannan muhimmin aiki ne da ya zama dole, don mu dauki matakin kwantar da hankalin mutanenmu, su yi hakuri da irin barazana da hasarar dukiyoyi da aka yi musu a dalilin zanga-zangar. Kamata ya yi a kyale su da mahukunta su yi maganinsu.
“Akwai mutanen da suka dade suna kulla makirci a boye dangane da wannan al’amari da ya shafi tsaron lafiyar al’umma, kuma aiki ne da ya shafi mahukunta su bankado mutanen su yi maganinsu tun kafin bakin alkalami ya bushe. Masu yunkurin kafa kasar Biyafara suna cewa, za su yaki duk mai adawa da hakan kuma za su kori duk ’yan Arewa mazauna Kudu maso Gabas. Muna sanar da su cewa, mu ba za mu yi yaki da su da zai kai ga zubar jinin miliyoyon jama’a ba gaira ba dalili ba, domin mun san irin barnar da aka yi a lokacin yakin basasa na shekarar 1967 da aka yi shekara uku ana yi ba. Ba za mu so a sake maimaita irin wannan barna ba. Wannan shi ne daidai lokacin da ya kamaci duk mai kishin Najeriya da kaunar zaman lafiya ya taimaka wajen bayar da gudunmawarsa ga shirin samar da zama lafiya da ci gaba da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi.”
Shi ma Shugaban Kasuwar Alaba International a Legas, Injiniya Paul Chijioke Okenwa, wanda dan asalin Kudu maso Gabas ne, bai goyi bayan fafutikar kafa kasar Biyafara da ake yi ba. Ya ce: “Dukkanmu ’yan Najeriya ne kuma duk mutanen da suka kyamaci salon mulkin da suke hangen an danne musu hakki, ya kamata a saurari bukatunsu ta hanyar tattaunawa da su domin shawo kan al’amarin cikin sauki ba tare da tashin hankali ba.
“A Najeriya akwai kabilu masu yawa da kowanne yake da bukatarsa wadda nake ganin kamata ya yi masu irin wadannan bukatu su kwantar da hankali wajen mika abubuwan da suke so kuma su jira sakamako daga mahukunta domin biyan bukata ta hanyar zubar da jini ba za ta yi maganin matsalar ba,” inji Injiniya Paul.
Ya ce: “Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban al’ummar Najeriya baki daya  ba shugaban wani sashi na kasa ba, kuma na yarda cewa akwai tsarin da ya tanadar wa kowane sashi ba tare da bambanta su ba. Idan muna ganin an danne mana hakki a sashinmu to ina tabbatar maka yana sane da hakan kuma zai dauki matakin maganin al’amarin.”