An bar garin Bomala a baya wajen kayan more rayuwa – Baba Lawan
Al’ummar kauyen Bomala da ke mazabar Garko, a Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun bukaci gwamnati ta waiwaye su kan abubuwan more rayuwa da suka rasa a yankin. Wanda ya yi magana da yawun mutanen Bomala, Malam Lawan Siraka, wanda aka fi sani da Baba Lawan, ya ce Bomala yanki ne da ya ci […]
Al’ummar kauyen Bomala da ke mazabar Garko, a Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun bukaci gwamnati ta waiwaye su kan abubuwan more rayuwa da suka rasa a yankin.
Wanda ya yi magana da yawun mutanen Bomala, Malam Lawan Siraka, wanda aka fi sani da Baba Lawan, ya ce Bomala yanki ne da ya ci gaba sosai cikin kankanen lokaci; amma ba su da abubuwan more rayuwa irin su asibiti da ofishin ’yan sanda; sai ’yan sa-kai suke taimakawa a yankin.
Baba Lawan, ya ce mafi yawan mutanen Bomala mutanen Karamar Hukumar Gombe ne da ci gaban gari ya tashe su ya mayar da su can sakamon ayyukan hanyoyi da aka rika yi da kuma yadda wadansu suka samu dama Allah Ya hore musu suka mallaki filaye a wajen suka gina gidajensu.
“Komawarmu wajen ya sa mun bar Karamar Hukumar Gombe; amma Karamar Hukumar Akko ba ta dauke mu mutanen Akko ba, hakan ne ya sa muke koka wa gwamnatin jiha a waiwaye mu,” inji shi.
Lawan Siraka, ya kara da cewa garin Bomala ba ya da asibiti ko da na sha-ka-tafi, babu hanya ba ofishin ’yan sanda da idan aka samu rikici za a je sulhu dole sai an shigo gari.
Ya ce rashin asibitin ya sa mutanen da ke cikin lunguna idan rashin lafiya ya same su kafin su je asibiti suna shan wahala; saboda rashin hanya. Ya ce asibiti sai sun je Kumo hedkwatar Karamar Hukumar Akko, wadanda suke kusa kuma su je asibitin Pantami.
Baba Lawan, ya ce al’ummar Bomala, na matukar bukatar hanya domin rashin hanyar ya sa suna fuskantar matsaloli iri-iri, don haka suna bukatar hanyar kwalta kamar yadda aka yi wa wasu unguwanni a kwaryar garin Gombe; saboda Bomala waje ne da ke da mutane masu yawa.
Ya ce mutanen Bomala sun zabi Gwamna Inuwa Yahaya; don haka yake roko a dawo musu da martabar masarautarsu daga Dagaci ta koma ta Hakimi, wadda gwamnatin baya ta yagalgala ta aka rage ta aka bai wa wani wanda Dagacin yankin ne ya ba shi wuri ya zauna, amma aka hada kai da shi aka ci amanar masarautar aka yanka masa wani bangare a matsayin Dagaci.
Baba Lawan, ya kuma yi kira ga sabuwar gwamnatin Gombe ta Alhaji Inuwa Yahaya, cewa ta duba wannan lamari a dawo da martabar masarsutar Bomala da Dauda Adamu Tafida yake jagoranta, don masarauta ce da ke yiwa gwamnati biyayya.
A bangaren makaranta; ya ce suna son a samar da babbar sakandare don ’ya’yansu su samu saukin karatu.
Daga nan sai Lawan Siraka, ya yi kira ga mutanen yankin Bomala su ci gaba da hada kai da bai wa Dagacinsu goyon baya don kare martabar masarautar da kuma ciyar da yankin gaba.