An bar jaki ana dukan taiki

karin wa’adin watanni shida kan dokar-ta-bacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya sake kakabawa jihohi uku na yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan ba ta ba kowa mamaki ba, domin kuwa an san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Abin da ya ba kowa mamaki kawai shi ne yadda zai ci gaba da yin amfani da […]

An bar jaki ana dukan taiki
An bar jaki ana dukan taiki

karin wa’adin watanni shida kan dokar-ta-bacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya sake kakabawa jihohi uku na yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan ba ta ba kowa mamaki ba, domin kuwa an san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Abin da ya ba kowa mamaki kawai shi ne yadda zai ci gaba da yin amfani da dokar-ta-bacin don biyan bukatun wasu iyayen gidansa ba tare da la’akari da tsananin ukubar da hakan ke jawo wa jama’ar wadannan jihohin ba. ‘Yan siyasa, musaman masu adawa da gwamnatin Jonathan da kuma jam’iyyar da ta kafa ta, na sukan lamirin wannan matakin da suke cewa ba zai tsinana komai ba, domin kuwa me bara ta yi balle bana?

A ganinsu za a ci gaba ne da batar da makudan kudaden da ake matukar bukatarsu don yi wa talakawa ayyukan da suka kamata wajen tsaurara matakan da za su kuntata masu, su kuma kara dulmuya su cikin mawuyacin halin da zai kawar masu da ‘yanci, ya kuma ~al~alta tsarin tattalin arzikinsu da hana su daman wanzar da zumunta tsakaninsu. A takaice dai masu lura da al’amuran yau-da-kullum na da’awar cewa akwai lauje cikin nadi game da karin wa’adin dokar-ta-bacin, kuma hakan bai rasa nasaba da yunkurin da ‘yan kudun da ke zagaye da Shugaba Jonathan ke yi don durkusar da Arewa da kuma hana jama’an cikinta rawar gaban hantsi a dukkan al’amurran da suka shafi harkokin mulki da tattalin arzikin kasar nan. Hakan kuma ya dugunzuma hankulan masu kishin Arewa don ganin cewa kayar da mage ba yanka ne ba domin ba haka ne mafita daga matsalolin da suka kai Arewa kasa ba.
An dauka cewa kwamitin sulhu da takadararrun kungiyar Boko Haram da Shugaba Jonathan ya kafa a watannin baya zai taimaka masa wajen gano bakin zaren warware wannan matsalar da ake cewa tana da alaka da addini, amma sai ga shi nan rahoton da ya mika bai gamsar da jama’a ba domin kuwa babu wani takamammen abu da ke cikinsa wanda ya nuna an samu wata nasara gagaruma. Baicin haka nan kuma a daidai lokacin da wannan kwamitin ya mika rahotonsa ne Shugaba Jonathan ya bayyana aniyarsa ta karin wa’adin dokar-ta-~acin. To idan haka ne kuwa ina ranar wancan kwamiti da kuma kokarin da askarawa suka yi cikin watanni shida don kawo karshen tashin-tashinar?
Tarzomar siyasa ko rikicin addini ba sabbin abubuwa ne ba, an dade ana fama da su a sassa daban-daban na kasar nan, ana kuma samun nasara a dukkan lokacin da aka tunkare su don magance illolin da suke hadasawa. To amma sai ga shi matsalolin da suka kunno kai a Arewacin kasar nan kusan shekaru goma sha uku da suka shude sun gawurta, sun buwaya, sun kuma fi karfin duk wata hukuma, domin kuwa ana cewa shugabanni kasar nan na da hannu wajen afkuwarsu da kuma kasaitarsu. Dalilin kuwa shi ne akwai kwakkwarar alaka tsakanin shugabannin Najeriya da na wasu kasashen ketare da ke sha’awar arzikin man fetur a bangaren Najeriya da ke gabar Tafkin Chadi, kuma kaman yadda ake yi a dukkan inda aka ce irin wannan albarkar ta bayyana a duniya, sai an yi mummunar gasar da kan haifar da kazamar gaba don cin gajiyar wannan arziki.
To irin wannan lamari na daya daga cikin ababen da suka haddasa rikice-rikice a yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya tun daga 2009, lokacin da wani kamfanin kasar China ya fara hakan man da aka samu akan iyakar Arewacin kasar Kamaru da Tafkin Chadi. An kuma tabbatar da cewa a wannan shekarar ce rikicin Boko Haram ya fara kamari, har hakan ya yi sanadiyyar yamutsin da ya jawo mutuwar daruruwan ‘ya’yan kungiyar a garin Maiduguri da Bauchi da wasu sassan yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan. Tun daga wannan lokaci ne kuma ayyukan ta’addanci suka ci gaba da wanzuwa a dukkan kasashen da ke yankin ga~ar Tafkin Chadi, wadanda suka fara cin moriyar man fetur din.
Bayyanar arzikin mai a ko ina alheri ne babba wanda kan iya rikidewa gagarumin bala’i. Shi ya sa arzikin mai a bangaren Nigeria da ke harabar Tafkin Chadi ya zamanto ma Najeria masifa wacce aka ce wai kamfanonin wasu kasashen waje, musamman Afrika ta Kudu da Faransa suke haddasawa don su samu sukunin hana abokan gogayyarsu, musaman ma kasar China, cin moriyar arzikin fiye da su. To a Najeriya ma haka abin ke kasancewa, arzikin man fetur din da aka gano ne a Tafkin Chadi ke sanya kamfanonin wasu kasashen waje kafa kungiyar ‘yan ta’adda, suna kuma samun goyon baya daga shugabanni da zimmar samun gudummawarsu don ci gaba da mulki. Ya kamata Gwamnatin Jonathan ta fahimci haka, ta kuma dawo daga rakiyar wadancan kasashen da ke hana tamu kasar zama lafiya, ta kuma daina barin jaki tana bugun taiki.