An bar jirgin SAS ya sauka a Maiduguri an hana Gwamna Shettima tashi

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta bude filin jirgin saman Maiduguri a Jihar Borno, bayan rufe shi a ranar 27 ga Yuni inda hana masu zuwa Umara da ke cikin filin tashi zuwa Saudiyya, kuma aka ce zai kwashe wata uku a rufe saboda dalilai na tsaro.Jami’an gwamnati da jama’ar jihar […]

An bar jirgin SAS ya sauka a Maiduguri an hana Gwamna Shettima tashi
An bar jirgin SAS ya sauka a Maiduguri an hana Gwamna Shettima tashi

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta bude filin jirgin saman Maiduguri a Jihar Borno, bayan rufe shi a ranar 27 ga Yuni inda hana masu zuwa Umara da ke cikin filin tashi zuwa Saudiyya, kuma aka ce zai kwashe wata uku a rufe saboda dalilai na tsaro.
Jami’an gwamnati da jama’ar jihar sun nuna rashin jin dadi hana kan hana maniyyata aikin Umara 276 a bana da suka fito daga jihohin Borno da Yobe, inda sai da suka yi takakkiya zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano, amma aka bude wa tsohon Gwamnan don wata bukata tasa, kuma rufewar ta hana Gwamna mai ci Alhaji Kashim Shettima tashi daga filin jirgin saman, tare da tilasta shi yin tafiya cikin jerin gwanon motoci daga Maiduguri zuwa Abuja.
Sanata Ali Modu Sherrif, ya sauka a filin jirgin saman inda dubban magoya bayansa da ’ya’yan Jam’iyyar PDP da daruruwan jami’an tsaro suka tarbe shi tare da raka shi zuwa gidansa da ke kusa da Barikin Giwa a birni Maiduguri.
Sanata Ali Sharif ya sauka ne a filin jirgin ne tare da masu rufa masa baya da suka hada da ’yan Majalisar Wakilai uku daga jihar wato Abdulrahaman Tereb da Peter Biye da Isa Kangar da tsohon dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Kashim Ibrahim Imam da tsohon shugaban Jam’iyyar ANPP na Jihar Alhaji Muhammed Imam da sauransu.
A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan da saukarsa a Maiduguri ya bayyana niyyarsa ta ficewa daga Jam’iyyar APC, inda ya ce: “Na lura Jam’iyyar APC ba jam’yya ce ta jama’a ba, kuma ba za ta kai labari ba, kuma kuna ganin yadda jama’a suka zo tarbarmu, duk da cewa ba yanzu ne za mu canja shekar ba sai bayan azumi. Yanzu mun zo ne kawai saboda mu tuntubi mutanenmu a kan niyyarmu ta canja shekar, kuma muna sa ran za mu sake dawowa domin mu komawa Jam’iyyar PDP, saboda ba mu gamsu da salon mulkin Gwamna Kashim ba, a da mun yi zaton mun kawo wa mutanen Borno kyakkyawan shugabanci, amma sai muka ga ba haka ba ne. Don haka mun shiga kunya, to amma yanzu za mu gyara kuskurenmu ta hanyar komawa Jam’iyyar PDP. Ba wai ina fada ne da Gwamna Kashim ba, a’a babu wani abin da ke tsakaninmu, kuma Allah ne Ya ba shi mulki.”
Tuni garin Maiduguri ya dauki wani sabon salon na lika hotunan tsohon Gwamna Ali Sherrif da mukarrabansa dauke da tutar Jam’iyyar PDP, yayin da ake lika hotunan Gwamna Shettima da tutar Jam’iyyar APC.