An bar mata a baya a bangaren ilimi – Hajiya Hafsat Mohammed Baba

Hajiya Hafsat Mohammed Baba ita ce Tsohuwar Shugabar Mata Ta Jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) sannan cikakkiyar ’yar kasuwa ce inda ta bude kamfanoni da dama.  Zinariya ta samu damar tattaunawa da ita a garin Kaduna inda suka tabo batutuwa da dama da suka hada tarihin rayuwarta da fadi-tashin da ta sha kafin ta […]

An bar mata a baya a bangaren ilimi – Hajiya Hafsat Mohammed Baba
An bar mata a baya a bangaren ilimi – Hajiya Hafsat Mohammed Baba

Hajiya Hafsat Mohammed Baba ita ce Tsohuwar Shugabar Mata Ta Jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) sannan cikakkiyar ’yar kasuwa ce inda ta bude kamfanoni da dama.  Zinariya ta samu damar tattaunawa da ita a garin Kaduna inda suka tabo batutuwa da dama da suka hada tarihin rayuwarta da fadi-tashin da ta sha kafin ta kawo wannan matsayi.  Ga tattaunawar kamar haka:

Zamu so mu san takadfaccen tarohin rayuwarki?
 Sunana Hajiya Hafsat Mohammed Baba. Ina zaune ne a Jihar Kaduna.   Na yi karamar makaranta, da babbar makaranta, da jami’a da kwasa-kwasai da dama.   Na yi Babbar Diploma (Post Graduate Diploma) akan Peace and Complete Resolution, sannan na yi karatun HND a kan Hotel and Catering Management sannan ina da PGD  a kan International Relations.  Na yi aiki a Health Management Board a Kaduna a Asibitin Barau Dikko.  Na yi aiki a Cibiyar Horar da Malamai, National Teachers Institute (NTI) da ke Kaduna.   Na bude Albarka Airlines Catering Serbices da dai sauransu.   Na shiga aikin sa-kai (NGOs) domin na taimakawa al’umma. Na fara yin wannan aiki da margayiya Laila Dogon Yaro, kan tallafawa mata da kuma tabbatar da cewa ana damawa da su a kowane fanni, daga baya na kafa nawa, wanda nake yi har yanzu mai suna, Global Initiatibe for women and Children don tallafawa mata da yara har karkara.  Muna aikin nan da kungiyoyin cikin gida da na waje kamar su European Union da Nigerian Herbal Reproductibe Health Initiatibe da Center for Integrated Health Project da dai sauransu.
Wane dalili ne ya sa kike wannan ayukkan sa kai?
 Saboda na ga mahimmancin taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa jama’a domin gwammanati kadai ba za ta iya yin komai ba.

Me za ki iya cewa da yanayin ilimin matan arewa?
Akwai cigaba, amma yawanci ba a cika sa yara mata makaranta ba musamman a karkara. Akwai bukatar a kara wayar wa iyaye kai kan ilimin mata shi ya sa, mu matan da Allah Ya ba hali muka tashi tsaye kan kafa kungiyoyi da dama don ganin mun shawo kan wannan matsalar domin kuwa kasar da mata ke baya a fagen ilimi ba za ta samu cigaba yadda ya kamata ba.   Misali idan kika je asibiti za ki ta jin korafi daga wasu mazajen su, amma kuma su ke hana ya’yansu mata su nemi ilimi su fito su taimaka wa jama’a.   Shi ya sa mukan jawo hankalin mutanen mu da cewa karatu ko kuma in ce ilimi shi ne ginshikin komai na rayuwa.

Wace hanya ce kike ganin idan an bi za a iya bunkasa ilimin mata?
To ni dai ina gamin gwamnati ta sa himma wajen gyara sha’anin ilimi, saboda a gaskiya mun samu tabarbarewar ilimi a kasar mu, ba kamar da ba lokacin da muka yi makaranta amma yau sai aka wayi gari abubuwa sun koma baya.   Ba kwararrun malamai da kayan aiki da dai sauran su wanda yanzu kam dole sai an yi gyara na musamman don shawo kan wannan matsalar. Kuma a cigaba da wayar da kan jama’a kan barin yara suna tallace- tallace, maimakon zuwa makaranta. Sannan  kuma dole mu sa hakuri kan duk abin da muke, saboda na lura cewa matan Arewa ba su cika jajircewa kamar yadda matan Kudu ke jajircewa ba.   Za ki ga ko tallafi aka kawo matan Kudu sun san hanyar da za su bi su amfana, suna da hakurin su juya taro zuwa kwabo, amma mu mun fi son mu zauna muna ta kashewa karshen ta a koma bara.

Ya kika ga siyasar mata?
Siyasar mata a nan arewa ya bambanta da na Kudu.  Idan kika kawo maganar addinin mu da al’adarmu da sha’anin ilimi za ki ga akwai bambanci matuka, amna duk da haka muna kokari yanzu.   Sai dai abin da zan kara anan shi ne duk wani abu da za mu yi, mu rike addinin mu da mutunci mu. Za mu ga Allah zai sa mana albarka.  Waman shi ne abinda zan ce wa matan arewa.   A matsayina na wacce daga cikin matan da ke kan gaba a siyasa mu zama madubi ga wadanda suke tasowa, saboda ya zama tilas mu taka namu rawa domin idan aka kawo abubuwa kan harkar mu su amfana.   Yanzu haka a Jihar Kaduna muna kokarin mu ga cewa wannan kudurin doka an sanya mata hannu, ya zan lallai idan mace ta je asibiti ta samu komai a kyauta. Bai dace a ce mace ta je asibiti amma a rika umartarta ta ta kawo wannan da wancan ba, hakan ke sa a wasu lokuta ake samun rasa rayuka a wasu lokuta.  Idan kika ziyarci wadansu kasashen duniya da suka ci gaba za ki tarar sun san mahimmancin mata da zamantakewar lafiyar su. Misali Boko Haram idan aka dubi sansanin ’yan gudun