An bar mata a baya a bangaren ilimi(4)( – Hajiya Hafsat Mohammed Baba
hijira wa za a tarar mata da yara. Yanzu yawancin su ma an bar su ba mazaje, ba abin yi. Idan akwai ilimi da sana’a, za a kai ga hurumin da su ma za su taka nasu rawa na tallafawa kansu. Za a fi samun karfi sosai. Wane cigaba kika samu ta dalilin wannan kungiyoyin […]
hijira wa za a tarar mata da yara. Yanzu yawancin su ma an bar su ba mazaje, ba abin yi. Idan akwai ilimi da sana’a, za a kai ga hurumin da su ma za su taka nasu rawa na tallafawa kansu. Za a fi samun karfi sosai.
Wane cigaba kika samu ta dalilin wannan kungiyoyin da kika kafa?
Na farko ina jin dadin ina daga cikin mutanen da ke ceto ran wasu ta hanyar tallafa musu. Kuma a yau ina daga cikin matan da ke wa gwamnati magana kan koke-koken ’yan uwa na mata har a samu biyan bukata. Mutane su amfana, wannan abin farin cikin ne matuka a wurina. Kuma ina ganin wannan yana daga cikin babban ci gaban da na samu, kuma irin wannan ayyuka sun kai ni kasashen duniya da dama, kuma a nan gida kadan ne cikin jihohin da ban taka ba.
Wadanne kalubale kika fuskanta ta dalilin wannan aiki?
Suna nan da yawa, wani lokacin mutane suna ganin cewa kana da kudi, suna zuwa don a ba su kawai su yi sha’anin gabansu. Sannan kuma ba su sani ba duk wata kungiya tana da tsarin bayar da taimako ba don kawai a rika kashewa ba. Amma yawancin mutane ba sa ganewa. Ko an tura kudi daga kasashen waje don tallafawa mutane. Akwai hanyoyin da ake bi don yin haka, uwa uba matsalolin auratayya, kafin mu maida hankalin ma’aurata kan hanya madaidaiciya sai mun sha wuya kuma muna yin haka ne da hadin guiwar Human Right Commission, WRAPA da dai sauransu, don samun maslaha.
Ya ki ke jin hada wadannan ayyuka da rayuwar aure?
Na samu saukin yin haka saboda na samu goyon bayan iyaye na da mijina. Babu abin da zan ce illa Alhamdulillahi. Abin da ba mu so shi ne mace ta nade hannu ta jira sai miji ya kawo. Da karfintki da lafiyar ki, ba sai kin fita ba mace za ta iya tsara rayuwarta. Ko tana zaune gida ne akwai sana’a da dama da za ta iya yi, wanda zai iya dara na masu aikin ma wajen samu. Don haka aure ba zai hana mu yin abin da za mu tallafawa kan mu ba. Mutuwar zucciya babbar matsala ce, shi ya sa kungiyoyin mu ba su da karfi kamar na ’yan Kudu, don ko gwamnati za ta taimaka mana ba za ta yi daidai ba. An fi son mu hada kai, don haka mu rika juriya don tallafawa kanmu, abu ne muhimmi.
Me kika fi so a rayuwa?
A gaskiya iyali na, da kuma taimakon mutane, don ni ba nan duniya na ke dubi ba, a’a ranar da zan tsaya gaban Allah shi nna sa a gaba.
Wace shawara gare ki ta musamman ga matan arewa?
Mu cire kyuya, mu cire rashin hakuri. Duk abin da za mu yi, mu yi saboda Allah da kuma sanin cewa muna taimakon kanmu ne. Mu kula da ‘ya’yan mu su daina gararamba, su daina yin sake. Sannan idan muna da ikon hana ’ya’yanmu yin bara ko yin tallace-tallace a kan tituna, to mu yi kokarin yin haka. Mu rika taimakawa na baya, don a samu ci gaba a kowane fanni. Sanaan a fannin siyasa, muna fatan mata za su rika jajircewa don a rika damawa da su, don idan muna jiran maza su ba mu, to ba za su taba bamu ba. Kuma yawan sake saken mata a Arewa ya yi yawa, wanda dole sai mun tashi tsaye don shawo kan wannan matsalar da kanmu, sannan mu mayar da hankali wajen ba ’ya’yanmu ilimin da ya dace.