An bayar da belin wanda ake zargi da yin garkuwa da ’yarsa

Wata Kotun Majistare da ke Masaukin Alhazai na Jihar Kano, ta bayar da belin mutumin da ake zargi da yin garkuwa da ’yarsa tare da neman kudin fansa daga mahaifiyarta wato matarsa. Tun dai a wancan zaman kotun, wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa inda kotu ta neme shi da ya […]

An bayar da belin wanda ake zargi da yin garkuwa da ’yarsa

Wata Kotun Majistare da ke Masaukin Alhazai na Jihar Kano, ta bayar da belin mutumin da ake zargi da yin garkuwa da ’yarsa tare da neman kudin fansa daga mahaifiyarta wato matarsa.

Tun dai a wancan zaman kotun, wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa inda kotu ta neme shi da ya kawo mutum biyu da za su tsaya masa wanda ya hada da dagaci ko kuma babban limamin yankinsa.

Mai Shari’a Sakina Aminu ta dage sari’ar zuwa ranar 9 ga watan nan don ci gaba da sauraren shari’ar.

Idan za a iya tunawa wata mata mai suna Shamsiyya Muhamamd wacce ita ce mahaifiyar yarinyar ’yar kimanin shekara hudu ta sanar da ’yan sanda cewa an yi garkuwa da ’yarta a ranar 29 ga watan Satumba, 2020 inda kuma daga bisani aka fara kiranta a waya ana neman ta biya Naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa ko kuma a kashe ta.

Bayan mako biyu ne da ’yan sanda suka gudanar da bincike sai suka gano cewa mijin matar ne wato mahaifin yarinyar, Fahad Ali yake wadannan kiraye-kiraye ta wayar hannu, inda kuma aka samu yarinyar da aka yi garkuwa da ita a tare da shi.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano