An bayyana asalin Sarautar Sarkin Gobirawa ta Katsina
Wasan barkwanci tsakanin Gobirawa da Katsinawa abu ne mai tarihi, Katsinawa na ganin su ne iyayen gidan Gobirawa saboda sun ci su da yaƙi har ake cewa da Gobirawan suka ga za a ƙarar musu da mutane sai suka yi furucin nan na “Amazaya” wato a juya ko a koma baya domin a samu waɗanda […]
Wasan barkwanci tsakanin Gobirawa da Katsinawa abu ne mai tarihi, Katsinawa na ganin su ne iyayen gidan Gobirawa saboda sun ci su da yaƙi har ake cewa da Gobirawan suka ga za a ƙarar musu da mutane sai suka yi furucin nan na “Amazaya” wato a juya ko a koma baya domin a samu waɗanda za su koma gida. An ce dalilin wannan ne aka samu sunan wani ƙauye da ke kan hanyar zuwa Jibiya. Ana kiran ƙauyen da suna Mazanya. Kazalika, an ce a wajen wannan yaƙi ne su Katsinawan suka ƙwace kyauren Gobirawan. Wasu na cewa har can garin Gobirawan aka ɗauko ƙyauren yayin da wasu ke cewa dama duk inda Gobirawan za su da wannan ƙyaure suke zuwa. Su kuma Gobirawan suna cewa, sato shi aka yi. Haka dai wannan wasan barkwanci yake gudana har zuwa yau.
Sarkin Gobirawan ya fara da bayar da taƙaitaccen tarihin gidansu har zuwa kan sa da yadda ya gaji ita wannan sarauta. “Mahaifina Alhaji Usman wanda aka fi sani da Mani Bagobiri, ya zo Katsina ne daga Sabon Birnin Gobir.
Yawon karatu ya kawo shi,kuma ya fito daga tsatson masarautar gobir a can Sabon Birni. Da ya zo Katsina yayi karatu a gidan Malam Falalu dake Darma,ya kuma zauna Adoro da sauran wasu wurare acikin garin Katsina.’’
Abin da yasa aka nada Mahaifina Sarkin Gobirawan Katsina
A lokacin da Mahaifina yaga ya fara kafuwa acikin garin Katsina sai ya fara tattara Gobirawa ’yan uwansa a inda yake. Yana yin karatu kuma yana sana’a.
Ya kuma ɗauki sana’ar sayar da babura da wasu sassansa, kuma ya fara wannan sana’a a nan wajen gidan su mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema kuma har yanzu ‘ya’ya da jikoki suna ci gaba da sana’ar a nan inda ya fara.
To zamansa a wannan wuri ya sa ya san mutane sosai saboda wannan sana’a domin a lokacin babu yawan babura. Sannan kuma duk wani baƙon Bagobiri da ya shigo Katsina to wajen mahaifina za a kai shi.
To ana cikin haka, sai wata rana wani amininsa tsohon soja ya ba shi shawarar cewa yana da kyau su kafa ƙungiyar Gobirawa mazauna Katsina, ya kuma ba shi hujjojin yin hakan. Marigayin sai ya ce shi da bai yi boko ba ya za a yi ya kafa ƙungiya? A ƙarshe dai aka kafa kungiyar kuma aka ba shi shugabancinta.
To lokacin da suke ƙoƙarin kafa ƙungiyar sun je wajen sarki domin shaida masa abin da suke ƙoƙarin yi. Marigayi Sarki Kabir ya yi na’am da wannan niyya ta su. A karshe sai Sarki ya ce a sanya shi cikin ‘yan ƙungiya, Sarki ya ce ai shi ma Bagobiri ne ta wajen kakarsa.
A haka dai aka rabu ana wasa da dariya. Sarkin Gobirawan na II ya ƙara da cewa, bayan an zaɓi mahaifinsa shugaban ƙungiyar Gobirawan ya kuma ci gaba da abubuwan da ya saba yi, wato ƙwato wa Gobirawa haƙƙinsu a inda aka zalunce su tare kuma da tabbatar da cewa an fitar da ɓata gari a cikinsu in ma har akwai, domin na san da wuya ka ji an ce ga ɓarawo Bagobiri; don ba mu da su sai fa in can daga dangin uwa Katsinawa ya koyo, domin su ne ɓarayi saboda har yanzu ƙyaurenmu da suka sato yana hannunsu,” inji Sarkin Gobirawa Kabir.
“Sai Sarkin Katsina Muhammadu Kabir ya ce wa mahaifina,wannan shugabancin ƙungiya ya yi maka kaɗan,na ba ka Sarkin Gobirawan Katsina. Duk inda nake Sarauta kai ma haka,wato tun daga Dankama har Damari. Ka ji yadda aka yi Mahaifina ya zama Sarkin Gobirawa na farko a masarautar Katsina.
Yadda Sarautar Gobirawa ta zo gare ni
Mahaifina ya ci gaba da mulkin Gobirawa har lokacin da Allah ya yi wa Mai martaba Sarki Kabir rasuwa, Allah Ya jiƙansa da rahama.
Bayan rasuwarsa aka naɗa Sarki na yanzu Alhaji Abdulmuminu Kabir,yau kimanin shekara goma da wasu ‘yan watanni. To bayan shekara uku da naɗa shi wannan Sarki Allah ya yi wa mahaifina Sarkin Gobirawa rasuwa.
Bayan mutuwar tasa sai dukkanmu muka ɗunguma muka nufi wajen Sarki domin mu yi masa ta’aziyya tun da Sarki Uba ne. To bayan mun gama gaisuwa sai Sarki ya ce, ina ‘ya’yan Sarkin Gobirawa? Aka amasa ga su nan,sai ya ce, to ku je ku fitar da Sarki acikinku ku zo in naɗa shi.
To bayan an dawo Gida aka fara shawarwari,ni da ma can harkar Almajircina ta fiye min komai saboda haka ban ma tsaya tunanin neman wata sarauta ba tun da akwai na sama da ni. Wani ƙanin mahaifinmu ya fito ya ce yana so, amma sai aka ce a bari har sai sauran danginmu daga can Sabon Birni sun zo.
Lokacin da su waɗannan dangi namu suka zo, sai suka ce kada a kashe gidan Sarkin Gobirawa Alhaji Mani, tun da yana da manyan ‘ya’ya a zabi ɗaya daga cikinsu a ba shi. Na dawo daga makaranta sai aka ce an tattauna kuma an yanke shawara ni aka zaɓa in zama Sarkin Gobirawa.
Hujjojin da aka ba da su ne; kowa yasan duk inda Alhaji za shi tare da ni yake zuwa, ni jama’ar Alhaji suka fi sani. Sai na ce musu a’a, domin akwai yayyena biyu kuma suna nan. Aka dai tsaya cewar ni ɗin dai aka zaɓa, to ka san sau da yawa Allah yakan yi hukuncinsa a lokacin da ya so.
To sai muka tashi muka nufi gidan Sarki domin ba mu san yadda ake yi ba. Da muka samu Sarkin Labarai na yanzu Alhaji Iro Yaro, Shine wanda ya nuna mana yadda ake yi,kai ƙarshe ma shi ne wanda ya rubuta mana takardar da ake rubutawa ta neman sarautar.
To bayan an rubuta takardar neman sarautar sai wajen sanya suna. Da shi Sarkin Labarai ya ji yadda sunan nawa yake, ya jinjina kafin ya rubuta saboda nauyin sunan ga shi sarkin da ita kanta masarautar.
Jin cewa Muhammadu Kabir Usman ne yake neman sarautar mahaifinsa, sai Sarki Abdulmumini ya ce a ce ba sai mun shigo ba, mu je an ba ni wannan Sarauta. Wani Dogari yana ba mu labari, ya ce kusan shekararsa hamsin a nan amma bai taɓa ganin bayar da sarauta irin tawa ba.’’
Shin za ka dora daga inda mahaifinka ya tsaya ko ka ɓullo da wata hanyar taka daban?
Sarkin Gobirawan ya ce “to kusan duk inda mahaifina ya tsaya daga nan na dora domin wasu abubuwan ma ni nake zuwa in yi su a maimakon sa saboda haka babu wani abin da ban sani ba ko ban koya ba.
Kai hatta masallacin da ya gina a nan kofar gidanmu kuma yake limanci, wani lokacin ni zai ce in zo in ja Sallar,.To duk ire-iren waɗannan hidimomin na dora a kansu.
Sannan kuma bayan naɗin sarautar kungiyarmu ta ɗan yi sanyi domin har akwai lokacin da wasu suka je gidan sarkin Katsina suna neman kafa ƙungiyar aka ce musu babu ƙungiya sai dai sarki, a wannan lokaci ni kuma ban daɗe da dawowa daga Sabon Birni ba.
Bayan na ji cewa ana son kafa ƙungiyar Gobirawa ta kasa, na tafi har Kano domin jin yadda za ta kaya. To wannan shi ne zan ce kawo wani abin da shi mahaifina bai kawo ba, wato sanya ƙungiyarmu ta nan Katsina cikin babbar ƙungiyar ta kasa.’’
Ko Sarkin Gobirawa ya taɓa wakiltar Masarautar Katsina?
“To ka san wakilci kamawa take, akwai wankan Sarauta da aka yi wa Sarkin Gobir na Madawa da ke cikin Jamhuriyyar Nijar, akwai wurare da dama inda na je na kuma sadu da sarakunan Gobirawa na ƙasashe da yawa” inji shi.