An bayyana dalilan da ke kawo rikicin manoma da makiyaya a Kudu

Wasu Fulani makiyaya da ke zaune a Jihar Kurosriba sun bayyana cewa tasirin da shugabancin kungiyoyin matasan kabilu ke da shi ne a yankunan Kudancin Najeriya ne ya sanya rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma ke kin ci da  cinyewa sakamakon, hadama da kwadayin abin duniya da matasan yankunan ke fama da shi.Fulanin da […]

An bayyana dalilan da ke kawo rikicin manoma da makiyaya a Kudu
An bayyana dalilan da ke kawo rikicin manoma da makiyaya a Kudu

Wasu Fulani makiyaya da ke zaune a Jihar Kurosriba sun bayyana cewa tasirin da shugabancin kungiyoyin matasan kabilu ke da shi ne a yankunan Kudancin Najeriya ne ya sanya rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma ke kin ci da  cinyewa sakamakon, hadama da kwadayin abin duniya da matasan yankunan ke fama da shi.
Fulanin da suka tattauna da Aminiya lokacin da aka yi taron musayar ra’ayi kan gano hanyar da za a bi domin samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a fadin Jihar Kurosriba da kuma sauran yankunan jihohin kudancin kasar nan sun hada da Malam Aliyu Abubakar, limamin Obanlikwu, wanda kuma makiyayi ne. Ya ce hanya daya da yake gani za a iya warware rikici tsakanin makiyaya da manoma duk da an san hakan na afkuwa jefi-jefi tsakanin Fulani da masu gona ko kuma iyaka-da iyaka walau ta jiha-da-jiha ko ta karamar hukuma shi ne hanyoyin da za a bi a gyara matsalar a yanzu.
“Duk da zamani ya canja ba daukar makamai ya kamata kowa ya yi ba, a’a mai gona kiran makiyayi zai yi ya ce ya zo ya ga irin barnar da shanunsa suka yi masa, a sasanta tun da babu wani Bafulatani da zai tura shanu gonar manomi da gangan domin yana faruwa cikin kuskure. Wani lokaci yara ne suke tare da shanu ba babban mutum ba ne, idan irin haka ya faru ba daukar doka a hannu ya kamata a yi ba.” In ji shi. Ya ci gaba da cewa idan aka gayyato mai shanu ya ba da hakuri, a fadi iya barnar da shanu suka yi, a kimanta, a biya mai gona daidai ta’adin da aka yi masa. Shi kuma Bafulatani kada ya ja fitina, ya ce ai na riga na biya barnar da na yi, domin a samu zaman lafiya.
Shi kuwa Alhaji Tanimu Adamu, ya shaida cewa son zuciya ce da matasan yankin kudu ke da ita ce, musamman yadda matasan kan kafa kungoyoyin matasan yankunansu, suna karbar haraji, wanda tasirinsu har ma ya nemi ya zarce na sarakunansu. “Domin idan Bafulatani ya zo kudu kiwo, kafin ya fara yin wani abu sai ya je ya ga basaraken yankin da ya sauka ya ba shi kudin jangali, sannan ma ya fara zuba shanunsa har ya tattaro iyalinsa ya zauna wannan wuri. To amma daga baya sai aka rika samun matasa suna kafa kungiyar matasa har ma tasirinsu yana nema ya zarce na sarakunansu; domin idan Bafulatani ya je ya ba sarki kudi, da zarar yaran sun gan su sai su ce waye ya ba su iznin yin kiwo? Idan ma har sun yi masu bayani sai matasan su nuna cewa su ma sai an sallame su, an ba su nasu kudin. kin ba su kudin da suka bukata ne ke haddasa rikicin alhali su Fulani ba su san wata kungiyar matasa ba, sarki suka sani. To wannan shi ne yake haddasa rikicin. Amma matukar ana son zaman lafiya, dole gwamnati ta tsame hannun matasa daga duk wani hukunci da ya ci a ce sarakuna ne suke zartarwa.”
Ya ce yau a Najeriya idan ana son a magance rikici tsakanin Fulani da manoma, dole fa sai an fada wa kai gaskiya. “Don zargin karya suke yi wa Fulani, don babu Bafulatanin da ya shigo wurin nan kiwo ba tare da izinin basaraken wurin ba. Sai ya biya su wasu kudade kafin ya zo ma ya kawo shanu.”
Waje daya kuma wakilinmu ya ji ta bakin Barista Musa Abdullahi Maigoro, mai baiwa Gwamnan Jihar Kurosriba shawara ta musamman kan harkokin baki, dangane da shawarwarin da wasu manoma suka bukata da idan an bi matakan za a samu zama lafiya da suka hada da korar Fulani makiyaya kwata-kwata daga jihar da kuma rika sarrafa ciyawa ana sayar masu, hatta shawarar shigo da shanu jihar daga kasashen waje ko arewa idan an kori makiyayan. Ya ce: “Abu ne wanda ba zai yiwu ba, domin kasar nan tsarin mulkinta ya bai wa kowane dan kasa ikon zama bisa zabinsa, inda yake so ya zauna. Rikici tsakanin Fulani da manoma abu ne wanda ya shafi kasa baki daya, ba rikici ne da ya shafi wani yanki ko jiha guda daya ba. Ba yadda za a yi a samu zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya sai dai a zauna teburin shawara, a fuskanci mene ne yake kawo rikicin tsakani, kowa kuma a kula da hakkinsa sannna kuma su makiyaya a yi masu tanadi na wurin kiwo, burtalai da shanunsu za su rika kiwo. karshe, ya kamata Gwamnatin Tarayya da na jihohi su kirkiro wasu tsare-tsare da za su kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.