An bayyana dalilin da APC ta lashe kujerar Gwamna a Ogun

Sakamakon nasarar da dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya samu, na lashe zaben Gwamnan Jihar, inda ya doke abokin karawarsa da ke samun goyon bayan Gwamna mai barin gado Ibekunle Amosun a Jam’iyyar APM, Abdulkabir Akinlade; jama’a da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan sakamakon […]

An bayyana dalilin da APC ta lashe kujerar Gwamna a Ogun

Sakamakon nasarar da dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya samu, na lashe zaben Gwamnan Jihar, inda ya doke abokin karawarsa da ke samun goyon bayan Gwamna mai barin gado Ibekunle Amosun a Jam’iyyar APM, Abdulkabir Akinlade; jama’a da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan sakamakon zaben.

A cewar Alhaji Musa Maitakobi, Shugaban Kungiyar Masu Motocin Haya ta RETAN, alhakin Shugaba Buhari ne ya kama Gwamna Ibikunle Amosun, inda dan takarar da ya tsayar ya gaza cin zaben jihar.

“Shugaba Buhari ya yi yakin neman zabensa a daukacin jihohin kasar nan, babu inda aka yi masa mummunar tarba in ban da Jihar Ogun. Shi Shugaba in ba Allah ba ne ya wulakanta shi, duk wanda ya wulakanta shi zai ga sakamakonsa. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa ka ga dan takarar Gwamnan ya sha kashi. Ai su mutanen jihar ba mahaukata ba ne,” inji shi.

Ya ce abin da ya kamata a mai da hankali a kai a yanzu, tunda an yi zabe a kaso mafi yawa na kasar nan shi ne addu’ar zaman lafiya ga kasa tare da fatan Allah Ya bai wa wadanda aka zaba ikon yi wa talakawansu adalci.

“Babu wani abin da yake yiwuwa in babu zaman lafiya kuma babbar ribarmu a wannan zabe da ya gabata shi ne samun shugabanni nagari, wadanda za su yi wa talakawansu adalci, su gabatar da ayyukan raya kasa domin ci gaban al’ummarsu. Muddin gwamnoninmu suka yi koyi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fannin jajircewarsa da gaskiya da rikon amana, to za a samu gagarumin ci gaba a shekara 4 masu zuwa,” inji shi.

Dan takarar gwamnan na APC a Jihar Ogun wanda ya lashe zaben duk da rashin goyon bayan da Gwamna mai ci a yanzu ya nuna masa, ya yi alkawarin kafa gwamnatin da za ta bai wa kowa hakkinsa ba tare da nuna wariya ko bangarenci ba. A daya bangaren dan takarar Gwamna na APM Abdulkabir Akinlade wanda ya samu goyon bayan Gwamna Amosun ya ki amincewa da sakamakon zaben, inda ya kudiri aniyar zuwa  kotu.

Shi dai Dapo Abiodun wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, a baya babban aminin Gwamna Amosun ne da tsohon Gwamnan Jihar Gbenga Daniel wadanda abokan juna ne, biyu daga cikinsu suka samu ikon zama Gwamna a jihar; kuma Dapo Abiodun ya bai wa Amosun gudunmawa a lokacin da yake neman zaben Gwamnan Jihar. Al’amura sun yi tsami ne a tsakaninsu lokacin da Dapo Abiodun ya nuna sha’awarsa ta zamowa Gwamna, sai ga shi Allah Ya tabbatar masa duk da rashin goyon bayan da tsohon aminin nasa ya nuna masa.