An bayyana dalilin rashin nada sarkin Agyaragu

Daraktan Gudanarwa na Jenkwe da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa, Mista Iliya Dagba Igube ya ce jinkirin da ake samu wajen nada Sarkin Agyaragu yana faruwa ne a sakamakon karuwar baki zuwa garin.Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke Agyaragu. Ya ce garin na daya […]

An bayyana dalilin rashin nada sarkin Agyaragu
An bayyana dalilin rashin nada sarkin Agyaragu

Daraktan Gudanarwa na Jenkwe da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa, Mista Iliya Dagba Igube ya ce jinkirin da ake samu wajen nada Sarkin Agyaragu yana faruwa ne a sakamakon karuwar baki zuwa garin.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke Agyaragu. Ya ce garin na daya daga cikin garuruwan da suke da yawan kaki, wadanda a cewarsa kodashike ba ’yan asalin jihar ne ba amma sun kwashe sama da shekaru 30 suna zama a garin. Wadannan mutane kabilu ne daban-daban da suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan kuma yawancinsu sun gina gidajen kansu suna kuma bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban garin da sauran yankin baki daya. Shi ya sa, a cewarsa aka kasa nada sarkin garin, sama da shekaru 30 ke nan da ta gabata.
Ya bayyana cewa: “Kamar yadda ka sani ne, a ko’ina a kasar nan idan baki suka zo wani gari da ba nasu ba kuma sai ya kasance wadannan baki suka fi asalin ’yan garin arziki ko a fannin ilimi ko yawa da dai sauransu, dole ne a samu jinkiri a batun sarautar garin. Domin idan an bar ainihin ’yan gari su nada sarki zai iya yiwuwa bakin ba za su amince da haka ba. Idan kuma aka ce baki su nada sarki, ba zai yi wa ’yan gari dadi ba. Shi ya sa a nata bangaren gwamnatin jihar ta riga ta ba al’ummar Koro damar nada sarkin Agyaragu da muke magana a kai don ta amince cewa garin Korawa ne muna da damar nada sarkinmu. Amma dayake Korawa masu son zaman lafiya ne, shi ya sa suna bin komai a hankali don kada ana dinke wani waje, wani waje kuma na yagewa. Shi ya sa har ila yau a bangarenmu jami’an gwamnati a wannan yanki, muna kokari wajen ba gwamnatin jihar nan shawarwari da suka dace, musamman game da yadda za a hada kan wadannan al’ummomi daban-daban, don a samu damar nada sarkin wannan gari ba tare da an samu tashin hankali ba.”
Daga nan sai ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba garin zai samu sarki. Domin a cewarsa, samun sarki a garin ba shakka zai jawo musu ci gaba a fannonin rayuwa fiye da yadda lamarin yake a yanzu.