An bayyana kulob din da za su hadu da Kano Pillars da na Enyimba a gasar zakarun kulob na Afirka

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta fitar da jadawalin gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Afirka (Champions League).  Jadawalin ya nuna kulob din Kano Pillars da ya lashe  gasar firimiya ta Najeriya zai kece raini ne da na Malakia FC da ke Sudan ta Kudu yayin da […]

An bayyana kulob din da za su hadu da Kano Pillars da na Enyimba a gasar zakarun kulob na Afirka
An bayyana kulob din da za su hadu da Kano Pillars da na Enyimba a gasar zakarun kulob na Afirka

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta fitar da jadawalin gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Afirka (Champions League).
 Jadawalin ya nuna kulob din Kano Pillars da ya lashe  gasar firimiya ta Najeriya zai kece raini ne da na Malakia FC da ke Sudan ta Kudu yayin da kulob din Enyimba kuma da ya zo na biyu a gasar zai hadu ne da na Buffles da ke Jamhuriyyar Benin.
Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta Pillars za ta yi tattaki zuwa Sudan ta Kudu ne a ranar 13 ga watan Fabrairun 2015 don fara wasa zagaye na farko yayin da wasa na biyu kuma zai gudana ne a garin Kano bayan makwanni biyu.  Ita kuma Enyimba tana gida ne a wasanta na farko a ranar 13 ga Fabrairun, 2015 inda za ta kece raini da kulob din Buffles yayin da makwanni biyu kuma bayan an yi wasan farko za ta ziyarci Jamhuriyyar Benin don yin wasa zagaye na biyu.