An bayyana matsalolin da ke haifar da cikas ga shari’a

An bayyana rashin iya aiki da kwadayi ko tsoro a matsayin abubuwan da ke janyo cikas a harkokin shari’a. Alkalin Alkalan Abuja, Mai Shari’a Ishak Bello ne ya bayyana haka a lokacin bukukuwan makon lauyoyi reshen Zariya na bana, wanda kungiyan lauyoyin ke gudanarwa a duk shekara. A ganawarsa da Aminiya jim kadan da kammala […]

An bayyana matsalolin da ke haifar da cikas ga shari’a

An bayyana rashin iya aiki da kwadayi ko tsoro a matsayin abubuwan da ke janyo cikas a harkokin shari’a.

Alkalin Alkalan Abuja, Mai Shari’a Ishak Bello ne ya bayyana haka a lokacin bukukuwan makon lauyoyi reshen Zariya na bana, wanda kungiyan lauyoyin ke gudanarwa a duk shekara.

A ganawarsa da Aminiya jim kadan da kammala bikin a babban dakin taro na Fabs Hotel, Mai Shari’a Bello ya ce: “Matsalollin da suke kawo cikas ko hana ruwa gudu a  harkokin gudanar da shari’u suna da dama, kuma matakan da ya kamata a dauka domin magance matsalolin su ne, a inganta dokokin da a yanzu sun riga sun zama na hana ruwa gudu saboda yanayi ya canza, zamani ya canza. Wadannan dokoki yanzu sun zama kasassu kuma sun zama abin kawo matsala a cikin aikin shari’a. Akwai wasu dokoki da yake ya kamata a canza su saboda dokokin suna nan ne tun lokacin Turawan mulkin mallaka, suna nan, ko jim kadan bayan sun tafi saboda haka nan dole ne sai an yi gyare-gyare a kan irin wadannan dokokin.”

Ya ci gaba da cewa a samar da kayan aiki ga ma’aikatan shari’a da kuma masu binceke da kuma su kansu masu gabatar da kara. “Domin kowanne ka dube shi yana fama da matsaloli, wadanda suke hana ruwa gudu a kan aikin shari’a. Domin idan bincike bai kyau ba, kuma ba a iya gama bincike  da wuri ba dole ne idan laifin da ba za a iya ba da beli ba ne, mutumin nan ya dingi zama a kurkuku ke nan,” inji shi.

Ya ce sai tsarkake zukata kuma an zage dantse wajen yin abin da ya kamata ga wadanda abin ya shafa, yayin magance matsalolin.

“Dole ne su fahimci cewa akwai matsaloli a kan wadannan rassa, domin komai zakewar mai shari’a da son ya yi aiki, idan ba a gama bincike ba ko kuma ba a gabatar da karar yadda ya dace ba, ba abin da zai iya yi. Saboda haka nan a takaice, wadannan su ne abubuwan da suke haifar da cunkoso a kurkuku amma a halin yanzu gwamnati ta dauki matakai na ganin cewa an rage cunkoso a gidajen yari, wanda ta kai ga ni kaina aka nada shugaba na kwamitin gudanarwa, wanda ya kunshi jihohi.

“Za mu zagaya kasar nan baki daya tare da hadin gwiwar  shuwagabannin kutona na jiha-jiha, domin mu ga cewa wadanda suka cancanci a sallame su, an sallame su nan take kuma daga cikin matakan da za mu dauka har da wanda aka tsare shi tsawon shekara biyar ba tare da an yanke masa hukunci ba, har in laifin sa bai dace da tsarewar ba.”

Daga karshe ya ce: “Kuma idan ka duba, wannan muhimmin al’amari ne da gwamnatin nan ta fito da shi, kuma na ga ta taka rawar gani. Idan muka samu hadin kai daga dukkan wadanda abubuwan suka shafa, na tabbata za mu kai ga nasara.”