An bayyana sunayen ’yan takarar shugabancin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Kotun Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta fitar da jerin sunayen ’yan takara 30 wda za su fafata a zaben Shugaban kasa wanda zai gudana a ranar 27 ga wannan wata.Kotun ta yi watsi da bukatar tsohon Shugaban kasar Francois Bozize, ta neman shiga takara a zaben. Hukumar ta yi hakan ne bisa dalilin cewa […]
Kotun Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta fitar da jerin sunayen ’yan takara 30 wda za su fafata a zaben Shugaban kasa wanda zai gudana a ranar 27 ga wannan wata.
Kotun ta yi watsi da bukatar tsohon Shugaban kasar Francois Bozize, ta neman shiga takara a zaben.
Hukumar ta yi hakan ne bisa dalilin cewa bai yi rajista da kundin zabe ba. Har ila yau, yana zaman gudun hijira ne a kasar Uganda sakamakon zargin haddasa kisan kare-dangin da ake yi masa. Baya ga shi kuma akwai Patrice Edouard Ngaissona madugun mayakan sa-kai na kungiyar Anti-Balaka wanda shi ma hukumar shirya zaben ta yi jifa da bukatarsa ta neman tsayawa takara. Wannan ya haifar da hatsaniya a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. inda tarin matasa magoya bayan Mista Ngaissona da kuma Mista Bozize suka kafa shingaye, suna yin kone-kone domin nuna fushinsu game da hukuncin da kotun ta zartar.
Sai dai rahotannin baya-bayannan sun tabbatar da cewa kusan komai ya lafa. Ofishin Jakadancin kasar Faransa ya bukaci jama’ar kasar su dakatar da zirga-zirga da suke yi a cikin birnin.
Hakazalika, Ministan Tsaron Faransa, Jean Ybes Ledriant ya ce dakarun kasarsa su 900 za su ci gaba da zama a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka har bayan kammala zaben wato lokacin da sabon Shugaban kasar zai kama aiki.
Faransa ta taba yi yunkurin cewa za ta rage adadin dakarunta daga 900 zuwa 700. Ganin barazanar da wasu kusoshi a kasar suke yi a yanzu na sake ta da zaune-tsaye ya sa ta soke wannan yunkuri. Har ila yau, akwai barazanar da Nourredine Adam yake yi daga gabashin kasar, inda yake so ya ga cewa wannan yankin ya balle ya koma karkashin kularsa. Hakan zai ba shi damar kafa wata sabuwar kasa da ya rada wa sunan Jamhuriyar Logone. Mista Adam shi ne madugun wani reshen hadakar kungiyar Seleka wadanda suka bai wa Michel Djotodia damar darewa kan kujerar mulki bayan kifar da Gwamnatin Francois Bozize.