An bindige ‘yan fashi uku a Ibadan

Rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ‘yan sanda (Operation Burst) da Gwamnatin Jihar Oyo ta kafa domin yaki da miyagun ayyuka ta yi nasarar dakile yunkurin fashi da makami a Otal din Emirate da ke Adegbayi a Ibadan a inda jami’an rundunar suka bindige uku daga cikin ‘yan fashin har lahira da kama biyu daga […]

An bindige ‘yan fashi uku a Ibadan

Rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ‘yan sanda (Operation Burst) da Gwamnatin Jihar Oyo ta kafa domin yaki da miyagun ayyuka ta yi nasarar dakile yunkurin fashi da makami a Otal din Emirate da ke Adegbayi a Ibadan a inda jami’an rundunar suka bindige uku daga cikin ‘yan fashin har lahira da kama biyu daga cikinsu.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai ba Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Mista Segun Abolarinwa wanda ya ce tawagar ‘yan fashin su shida ne suka kai hari zuwa Otal din Emirate dake unguwar Adegbayi a ranar Lahadi da ya wuce.

Ya ce, mazauna unguwar ne suka yi ta kiran layin wayoyin rundunar ta (OB) suna bayyana masu irin fargabar da suke ciki a lokacin da ‘yan fashin suke kokarin shiga cikin Otal din. Jami’an rundunar sun amsa kiran tare da hamzarta daukar matakin tunkarar ‘yan fashin tun kafin su kai ga aikata danyen aikin nasu.

“A daidai wannan lokaci ne jami’an rundunar suka bude masu wuta da harbin bindiga inda a nan take suka harbe uku daga cikinsu sannan suka kama biyu daga cikinsu sai kuma ragowar daya wanda ya tsere da harbin bindiga a jikinsa’ inji Abolarinwa wanda ya yi kira ga dukkan asibitoci na gwamnati da masu zaman kansu su taimaka wajen tona asirin irin wadannan mutane da suke ziyartarsu dauke da harbin bindiga a jikinsu.

Da yake karin haske a kan nasarar da rundunar ta samu sai ya ce, “yau mako uku da suka wuce kenan da wadannan ‘yan fashi suka hana mutanen unguwar Adegbayi sakat wajen yawan kai musu hare-hare da kwace masu dukiya. Saboda haka muke kira ga sauran jama’a dake zaune a Jihar Oyo da su yi koyi da mutanen wannan unguwa ta fannin hanzarta buga wayoyin jami’an rundunar ta (OB) a duk lokacin da irin haka ta auku gare su.”