An binne biliyoyin kudin sata a gonaki – Yakubu Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara ya ce wadansu mutane da suka sace dukiyar jama’a sun turbude su a cikin gonaki, inda ya ce yanzu haka jami’an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun fara tono irin wadannan kudi a cikin gonakin a kusa da Abuja.Barista Yakubu Dogara, ya shaida wa wasu manema labarai […]

An binne biliyoyin kudin sata a gonaki – Yakubu Dogara
An binne biliyoyin kudin sata a gonaki – Yakubu Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara ya ce wadansu mutane da suka sace dukiyar jama’a sun turbude su a cikin gonaki, inda ya ce yanzu haka jami’an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun fara tono irin wadannan kudi a cikin gonakin a kusa da Abuja.
Barista Yakubu Dogara, ya shaida wa wasu manema labarai a Legas a ranar Asabar da ta gabata cewa, ya kadu sosai da gagarumar satar kudin talakawa da aka gudanar a kasar nan a baya, wadanda hukumomin yaki da cin hanci suke bankadowa inda ya kawo misali da Naira biliyan daya da rabi da aka gano binne a wata gona a Abuja.
Barista Yakubu Dogara ya ce an tono Naira biliyan daya da rabi a gonar wani babban mutum a kusa da Abuja, inda ya nuna takaicinsa kan yadda wadansu mutane suke satar kudin da ba su bukatarsu a rayuwa.
Ya ce wannan gona yanzu haka jami’an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suna can suna kwashe kudin daga cikinta.
Barista Dogara ya ce bai taba ganin irin wannan tabargaza ba, inda mutane “suke sata don kawai jin dadin satar,” inda ya koka kan sabuwar dabarar barayin gwamnatin ta binne kudi a ciki gonaki.
“Idan aka kama ni aka kai gaban kotu kuma aka iya kwato wasu kudi a karshe babu abin da zai faru, mutane da dama ba za su ji shakkar yin almundahana da cin hanci da rashawa a nan gaba ba. Idan ka dubi mahaukaciyar satar dukiyar gwamnati da aka yi (hakika na kasance a cikin gwamnati na tsawon lokaci),  ban taba ganin irin wannan almundaha da muke gani a yau ba, inda mutane suka sace kudin da suka kai biliyoyin suka binne su a gonakinsu ba,” inji Dogara.
Yakubu Dogara ya ce hatta hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun kadu da irin dimbin kalubalen da yake gabansu game da yaki da almundahanar da suke yi.
“In da ku ne kuke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa dole hankalinku zai tashi sakamakon muguwar barnar da aka tafka,” inji shi.
Dogara ya kuma musanta zargin da ake yi cewa yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari ana yi ne da nufin muzguna wa bangaren adawa inda ya ce akwai na hannun daman Shugaban kasa da a halin yanzu ake tuhumarsu kan rashawar.