An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina
Marigayin ya rasu a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi tare da matarsa.
An yi jana’izar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a Jihar Katsina, bayan ya rasuwar da ya yi a hannun ’yan bindiga.
An binne shi ne kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
- Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa
- Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro
’Yan uwa, manyan jami’an soji, jami’an gwamnati da jama’a da dama ne suka halarci jana’izar marigayin.
An sace Janar Rabe da matarsa ne a ranar 30 ga watan Mayu a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
A lokacin jana’izar, mutane sun yi karatun Alkur’ani da addu’o’i tare da tunawa da irin hidimar da ya yi wa Najeriya.
Mutane da dama sun nuna baƙin cikinsu tare da takaici ne yadda mutumim da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare ƙasa ya mutu a hannun ɓarayin daji.
Jama’ar Katsina sun kuma nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro, inda suka ce rashin tsaro na ci gaba da shafar talakawa da kuma tsoffin jami’an tsaro.
Wani mazaunin yankin, Dokta Sama’ila Balarabe, ya ce wannan babban rashi ne ga jama’ar jihar baki ɗaya.
Ya ce Janar Rabe ya yi wa ƙasa hidima bisa gaskiya kuma bai cancanci irin wannan ƙaddara ba.
A cikin wata sanarwa, Hedikwatar Tsaro ta bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen soja wanda ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda.
Sojojin sun ce jajircewarsa za ta ci gaba da zama abin koyi ga dakarun Najeriya.
Sojoji sun kuma ce za su ci gaba da ƙoƙari wajen kama waɗanda suka sace shi da matarsa tare da murƙushe ƙungiyoyin ’yan ta’adda a ƙasar.
A gefe guda, ’yan Najeriya da dama sun yi martani kan lamarin, musamman a shafukan sada zumunta.
Wasu sun nuna damuwa kan tsaron ƙasa, suna cewa idan har Janar mai ritaya zai iya rasa ransa ta irin wannan hanyar, to talakawa babu wanda zai ba su kariya.
Sun buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar ta’addanci da ’yan bindiga.