An binne mutum 80 bayan harin jirgin soji kan masu Mauludi
Mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin bom da jirin sojin kasan Najeriya ya kai wa masu taron Mauludi sun tabbatar da yin jana’izar sama da mutum 80.
Mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin bom da jirin sojin kasan Najeriya ya kai wa masu taron Mauludi sun tabbatar da yin jana’izar sama da mutum 80.
Mazauna kauyan Tudun Biri sun shaida wa Aminiya cewa wasu gawarwakin ma a cikin buhu aka saka su aka yi musu jana’iza.
Wani mazaunin yankin mai suna Liman ya ce sun binne sama da mutum 90, wasu a cikin buhu.
Ya ce akwai wani magidanci da ya rasa matansa biyu da yaya, sai jariri daya da ya tsallake rijiya da baya a harin.
- Magidanta 340 sun sha duka a hannun matansu a Legas
- Jirgi ya jefa wa masu taron Mauludi bom a Kaduna
Wani mazauna yankin kuma, wanda ya samu tsira daga harin, Bello Shehu Gara, ya tabbatar da cewa jirgin sama ne ya jefa masu bon suna tsakiyar bikin Maulidi a garin.
“Muna cikin bikin Maulidi ne sai muka hangi jirgin na shawagi a sama, kafin mu ankara sai kurum ya sako bom wanda ya halaka mutum kusan 57.
“Sai muka hangi wasu na neman taimako, mun kai masu dauki, kurum sai jirgin ya sake sako wani bam din, daga Nan muka gudu,” inji shi
Ya ce sun yi jana’izar mutum akalla 74 da safiyar Litinin, banda gawarwakin da aka zuba a cikin buhu aka binne.
Ya kara da cewa akwai mutum 66 suka raunata da aka kai su asibitin Barau Dikko da ke garin Kaduna domin samun kulawa.
“Wannan ba shi ne karon farko da muke Mauludi a garin ba da daddare, domin ko a makon jiya mun yi Maulidi kuma babu abin da ya faru, sai a wannan karon,” in ji shi.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta dauki alhakin harin, wanda ta ce jirginta ne ya kai harin kan fararen hula bisa kuskure a lokacin da yake sintirin yaki da ’yan ta’adda.
Yankin Tudun Biri dai na kusa ne hanyar Birnin Gwari, a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da matsalar hare-haren da ke wa mutane kisan gilla da kuma garkuwa da su domin karbar kudin fansa.