An binne mutum biyun da ’yan bindiga suka kashe a Sanga

A ranar Litinin ce aka yi jana’izar wadansu mutum biyu, Ibrahim Manzo mai shekara 76 da Barnabas Musa, mai shekara 45 da wadansu ’yan bindiga suka kashe a kauyen Ambe Madaki da ke masarautar Numana a Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna. Mutanen, kamar yadda majiyar Aminiya ta ce  an kashe su ne ta harbin bindiga […]

An binne mutum biyun da ’yan bindiga suka kashe a Sanga
An binne mutum biyun da ’yan bindiga suka kashe a Sanga

A ranar Litinin ce aka yi jana’izar wadansu mutum biyu, Ibrahim Manzo mai shekara 76 da Barnabas Musa, mai shekara 45 da wadansu ’yan bindiga suka kashe a kauyen Ambe Madaki da ke masarautar Numana a Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna.

Mutanen, kamar yadda majiyar Aminiya ta ce  an kashe su ne ta harbin bindiga a ranar Lahadi da misalin karfe goma na dare a gidansu.

“Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne gidan kawai suka tunkara inda suka kashe mutum biyu da suka tarar a ciki ba tare da sun taba kowa ba kuma ba su kona gidan ko su dauki wani abu a ciki ba,” inji majiyarmu.

An gudanar da jana’izar ce a karkashin kulawar sojoji da sibil difens da sauran manyan garin.

Karamar Hukumar Sanga tana daya daga cikin kananan hukumomin da ake yawan samun kashe-kashe a Kudancin Kaduna inda ta kasance daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ke karkashin kulawar rundunar tsaron tabbatar da zaman lafiya ta ‘Operation Sabe Haben’ da ke da hedkwata a Jos, Jihar Filato.

 

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara

Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama

Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano