An binne Sanata Wakili a Abuja

  Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rage Talauci, Sanata Malam Ali Wakili na jam’iyyar APC daga jihar Bauchi wanda ya rasu jiya yana da shekaru 58 an binne shi a Abuja.   An binne marigayi Wakili wanda ya rasu a gidansa na Abuja kamar yadda addinin musulunci ya tanada a makabartar unguwar Gudu da misalin […]

An binne Sanata Wakili a Abuja

 
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rage Talauci, Sanata Malam Ali Wakili na jam’iyyar APC daga jihar Bauchi wanda ya rasu jiya yana da shekaru 58 an binne shi a Abuja.
 
An binne marigayi Wakili wanda ya rasu a gidansa na Abuja kamar yadda addinin musulunci ya tanada a makabartar unguwar Gudu da misalin karfe 3 na yamma kuma an yi jana’izarsa a babban masallacin garin Abuja.
 
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Gwamnoni da ’yan Majalisa da Sanatoci da shugaban hukumar DSS, Lawal Daura da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci jana’izar tasa.
 
Marigayi Wakili shi ne dan majalisar dattawa na biyu da ya rasu a wannan majalisar. Na farko shi ne tsohon gwamnan jihar Osun, Isiaka Adeleke ya rasu shekarar da ta gabata.