An binne sarauniyar kyau Ighodalo

An binne tsohuwar sarauniyar kyau a Najeriya Ibidun Ighadalo,  mai dakin baban mai wa’azin Kirista na cocin Tiriniti, Fasto Ituah Ighodalo, a ranar Asbar 20 ga watan Yuni a Legas. Aminiya ta kawo rahoton rasuwar marigayiyar mai shekaru 39, wadda ta rasu a ranar Lahadi 15 ga watan Yuni, bayan ta yi fama da ciwon […]

An binne sarauniyar kyau Ighodalo

Marigayiya Ibidun Ighodalo tsohuwar sarauniyar kyau

An binne tsohuwar sarauniyar kyau a Najeriya Ibidun Ighadalo,  mai dakin baban mai wa’azin Kirista na cocin Tiriniti, Fasto Ituah Ighodalo, a ranar Asbar 20 ga watan Yuni a Legas.

Aminiya ta kawo rahoton rasuwar marigayiyar mai shekaru 39, wadda ta rasu a ranar Lahadi 15 ga watan Yuni, bayan ta yi fama da ciwon zuciya a lokacin da ta yi bulaguro domin yin wani aiki a garin Fatakwal babban birnin jihar Ribas.

Kadan daga cikin manyan bakin da suka halarci jana’izar marigayiyar sun hadar da Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu wanda ya kuma wakilci Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki. Hakazalika Fasto Idowu Oluyomade mataimaki na musamman ga shugaban Cocin Ridim ya wakilci shugaban cocin Fasto Enoch Adebayo a wajen jana’izar.

Masu aikin binne gawa dauke da gawar tsohuwar sarauniyar kyau Ibidun a cikin akwati a lokacin bikin binne ta

Tuni dai shugaban Najeriya   Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar ta hannun mai magana da yawunsa Femi Adeshina.

Hakazalika babban attajiri mafi kudi a Afirka, Aliko Dangote ya ziyarci gidan mijin marigayiyar da ke Legas inda ya yi masa ta’aziyyar rashin da ya yi na mai dakinsa.

Dangote ya yi yawo da mota ba dare da jami’an tsaro ba.

Wani abin da ya dauki hankalin jama’a game da ziyarar da Dangoten ya kai shi ne, yadda ya tuka motarsa da kansa  ya isa gidan Fasto Ituah Ighodalo ba tare da direbansa ba ko wani dogari ko jami’in tsaro da ke ba shi kariyar tsaro ba.

A wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta an ga Aliko Dangote ya isa gidan fasto Ituah Ighadalo a cikin wata mota mai launin toka kirar G-Wagon da ya tuka da kansa.

Mijin Marigayiyar Fasto Ituah Ighodalo tare da yayansa Kaka da Zena a lokacin jana’izar a yankin Ikoyi a Legas

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara