An binne shi tare da motarsa
Ya sanar wa iyalinsa cewa, yana son a binne shi da motar don ya tuka ta a Lahira.
Wadansu iyalan mamata sun yi yakinin cewa, duk mai rai ba zai tafi da abin duniya cikin kabari ba don ya amfana.
Amma wani mutum dan kasar Meziko ya yanke shawarar yin watsi da wannan batu, inda ya bukaci a binne shi da babbar motarsa mai daraja da yake kauna.
- Najeriya A Yau: Dalilan kara kudin motar haya lokacin bukukuwa a Najeriya
- Ballon d’Or: Messi ya lashe Gwarzon Dan Kwallon Duniya karo na 7
Mutumin mai suna Don Adán Arana daga birnin Puerto San Carlos, a Jihar Baja California Sur da ke Meziko, bayan ya yi ta fama da wata cuta da sa shi yanke tsammanin rayuwa, ya kasa jin dadin motar da dansa ya ba shi ba da dadewa ba.
Ya yi hasashen cewa, ba zai dade ba a duniya saboda ciwon, don haka ya sa ya sanar wa iyalinsa cewa, yana son a binne shi da motar, don ya tuka ta a Lahira.
Mutunta wasiyyar karshe, lamari ne mai matukar muhimmanci a Meziko, saboda haka aka binne Don Adán Arana a cikin babbar motar da yake kauna.
Hotunan binne mutumin sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta na Meziko tare da nuna yadda ake amfani da mota mai kugiya domin saukar da motar mamacin a cikin kabarin da aka gina masa na bulo, inda aka ajiye akwatin gawarsa a kan kujerar motar.
Wakilin al’ummar yankin, Francisco Tobar ya bayyana wa kafar labarai ta El Universal, cewa “Dangin mutumin suna iya fuskantar tara mai yawa, saboda ba su nemi izini ba don binnewar da ba a saba ganin irinta ba.
Kamar yadda binnewar ta zama abin mamaki, haka yadda aka binne mamacin a cikin mota ya zama wani sabon abu da ba a saba gani ba.
A bara mun yi rahoto game da wani dan siyasar Afirka ta Kudu wanda aka binne shi a cikin abin kaunarsa mota kirar Mercedes limousine, a maimakon akwatin gawa na yau da kullum.