An binne wani attajiri da motarsa da gwala-gwalai na Dala miliyan 2
An binne wani attajiri mai suna Sheron Sukhedo dan kimanin shekara 33 da aka kashe bayan an harbe da bindiga a kusa da gidansa da ke kan layin Caroni Sabannah a kasar Trinidad $ Tobago da motarsa da gwala-gwalai da jimillan kudinsu ya kai Dala miliyan 2. Shi dai wani matashin attajirin, wanda ke kasuwancin […]
An binne wani attajiri mai suna Sheron Sukhedo dan kimanin shekara 33 da aka kashe bayan an harbe da bindiga a kusa da gidansa da ke kan layin Caroni Sabannah a kasar Trinidad $ Tobago da motarsa da gwala-gwalai da jimillan kudinsu ya kai Dala miliyan 2.
Shi dai wani matashin attajirin, wanda ke kasuwancin gidaje an binne shi da wadannan ababen more rayuwa ne da tunanin ko zai bukace su a rayuwar barzahu.
Attajirin ya mutu ya bar ‘ya’ya biyu, sannan kuma ya bar dukiya mai tarin yawa ga matarsa da ‘ya’yansa.
A cikin akwatin gawar, an sanya masa takalmi kirar Timberland da yake yawan sakawa lokacin yana raye a kusa da kafarsa, sannan kuma aka zuba masa kyaututtuka da ya samu a lokacin rayuwarsa.
An sanya masa fararen kaya sannan aka masa ado da sarka da zobe na gwala-gwalai a hannunsa da wuyarsa, sannan kuma an sanyasa ne a cikin akwatin Dala dubu 50, inda aka yi rubuce-rubuce kamar su Sheron’s Auto da World Boss a jiki.
Bayan an binne matashin attajirin a gidansa da ke Lambun Orchards da ke Chaguanas, daruruwan mutane sun ta zuwa domin taya iyalan mamacin jimamin rashin dan kasuwan. An ta nunawa tare bayyana tarihin mamacin ta hanyar bayyana motocinsa da yadda yake yawan amfani da gwala-gwalai da kuma wasa da mota.