An binne ’yan Maulidi 16 wasu 150 sun ɓace bayan hatsarin kwalekwale

An yi jana’izar mutum 16 a yayin da ake neman wasu sama da 150 daga cikin masu zuwa Maulidi da hatsarin kwalekwale ya rutsa da su a yankin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja. Kimanin mutum 150 sun ɓata a ruwa bayan kwalekwalen ya kife da su a yayin da suke tafiya taron Maulidi a […]

An binne ’yan Maulidi 16 wasu 150 sun ɓace bayan hatsarin kwalekwale

An yi jana’izar mutum 16 a yayin da ake neman wasu sama da 150 daga cikin masu zuwa Maulidi da hatsarin kwalekwale ya rutsa da su a yankin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja.

Kimanin mutum 150 sun ɓata a ruwa bayan kwalekwalen ya kife da su a yayin da suke tafiya taron Maulidi a yankin Gbajibo na ƙaramar hukumar.

Hukumomin jihar suun bayyana cewa mutanen su 300 da suka hada da mata da kananann yara sun hau kwalekwalen ne daga garin Mundi zuwa Gbajibo.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta sanar cewan an yi nasarar ceto 150 daga cikin matafiyan da lamarin ya rutsa da su.

Ta ƙara da cewa hatsarin ya auku ne a kusa da yankin Gbajibo, inda mutanen za su sauka.

Ta bayyana cewa in banda ’yan kaɗan daga cikin fasinjojin, yawancinsu Fulani ne daga ƙauyen Mundi.

Shaidu sun bayyana cewa hatsarin kwalekwalen ya sa an soke taron Maulidin da suke hanyar zuwa.

Hukumomi sun danganta hatsarin kwalekwalen da ɗaukar lodi fiye da kima a yayin da mazauna suka bayyana cewa abin ya faru ne bayan kwalekwalen ya yi karo da itatuwa a cikin ruwa.

Sun ƙara da cewa yanayin da abin ya auku na da ɗaure kai, ganin yadda jirgin ya rabe gida biyu alhali ba cike yake da mutane ba.

Wani wanda ’yan uwansa bakwai ke cikin fasinjojin kwalekwalen, Mudasir Abdulmumin, ya ce an ceto ’yan uwansa mata huɗu, ragowar ukun kuma sun rasu a hatsarin.

Ya ce in banda ’yan uwansa da ke hanyarsu ta komawa gida daga taron suna, sauran fasinjojin sun fito ne daga Mundi za su je Maulidi Gbajibo.

“Masu jirgi sun ce jirgin mai ɗaukar fasinja 500 ne, amma mutane 300 ne a cikinsa a lokacin.

“Abin mamaki shi ne jiragen rabewa ya yi gida biyu, ba tare da wani abu ya taɓa shi ba.” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa an yi jana’izar mutanen da aka riga aka gano gawarwakinsu.