An binne mutum 8 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina

Maharan sun jikkata wasu tare da sace wasu mutum biyu a yankin.

An binne mutum 8 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina

Akalla mutum takwas aka binne bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.

Ya bayyana cewa wadanda aka kashe duk mazauna kauyen ’Yan Gayya ne kuma an binne su ne da safiyar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Aminiya cewa, zugar ’yan ta’addan sun kai wa mutanen hari ne a hanyarsu ta dawowa daga kauyen Kukar Babangida zuwa ’Yan Gayya.

Wasu mutum hudu sun jikkata, wasu biyu kuma sun bace a sakamakon harin da aka kai a daren Lahadi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi karin bayani ba.

“An kashe mutum takwas, hudu sun jikkata, wasu biyu kuma ’yan ta’addan sun sace su. Zan yi karin bayani daga baya,” in ji shi.

Jibiya na kan iyakar Najeriya da Nijar. Karamar hukuma ce da a Jihar Katsina ta yi iyaka da kananan hukumomin Batsari, Kaita, Katsina, Batagarawa da kuma Zurmi da ke Jihar Zamfara.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe