An biya Naira miliyan 1.5 kafin a sako sarkin mafarauta a Osun

An sako sarkin mafarautan Ibokun, Amusa Dunsin, da ke hedkwatar karamar hukumar Obokun jihar  Osun, wanda aka yi garkuwa da shi ranar Litinin tare da wata mata suna Misis Tayo George, an sako su ne bayan an biya kudin fansa na Naira miliyan 1.5 da masu garkuwan suka bukata. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, a […]

An biya Naira miliyan 1.5 kafin a sako sarkin mafarauta a Osun

Masu garkuwa da mutane

An sako sarkin mafarautan Ibokun, Amusa Dunsin, da ke hedkwatar karamar hukumar Obokun jihar  Osun, wanda aka yi garkuwa da shi ranar Litinin tare da wata mata suna Misis Tayo George, an sako su ne bayan an biya kudin fansa na Naira miliyan 1.5 da masu garkuwan suka bukata.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, a yanzu haka Sarkin mafarautan da ake wa lakabi da Tirimi–Ode  da Misis George duk su na tare da iyalansu yanzu haka.