An biya Naira miliyan 5 kafin a sako ma’aikacin Taraba daga masu garkuwa
An sako babban ma’aikacin gwamnatin jihar Taraba Alhaji Yahaya Lau, bayan ya yi kwana uku a hannun masu garkuwa da mutane. Majiyarmu ta gano cewa, sai da aka biya masu garkuwa da Alhaji Yahaya kudi Naira Miliyan 5 kafin su sako shi. `Yan uwan Alhaji Yahaya sun kai kudin ne wani daji kusa da kauyen […]
Masu garkuwa da mutane
An sako babban ma’aikacin gwamnatin jihar Taraba Alhaji Yahaya Lau, bayan ya yi kwana uku a hannun masu garkuwa da mutane.
Majiyarmu ta gano cewa, sai da aka biya masu garkuwa da Alhaji Yahaya kudi Naira Miliyan 5 kafin su sako shi.
`Yan uwan Alhaji Yahaya sun kai kudin ne wani daji kusa da kauyen Kwando a karamar hukumar Ardo-Kola da ke jihar Taraba da misalin karfe 10:30 na dare.