An boye hodar Iblis ta N72bn a jikin keken guragu

Kimar hodar Iblis din za ta kai Yuro miliyan 1.4.

An boye hodar Iblis ta N72bn a jikin keken guragu

Kujerar Guragu da aka boye hodar iblis a cikinta

Jami’an ’yan sanda sun gano wata hodar Iblis da ta kai fam miliyan 1.2 (kimanin Naira biliyan 72) da aka boye a jikin keken guragu a kasar Italiya.

Wani karen ’yan sanda ne a filin jirgin saman Malpensa da ke Milan, babban birnin Italiya ya taimaka wa ’yan sandan wajen gano inda aka boye ta.

Mutumin da yake amfani da keken guragun ya nuna kansa a matsayin nakasasshe, kuma ’yan sandan da ke aiki a filin jirgin saman sun gano hodar Iblis din ce cushe a jikin keken.

Nan take ’yan sandan suka kama mutumin, wanda yabiyo jirgin da ya taso daga Jamhuriyar Dominikan, kasar da ake amfani da ita wajen safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Italiya.

Lokacin da karen ya ja hankalin ’yan sandan kan keken guragun, sun duba kayan da mutumin ke dauke da su amma ba su ga komai ba.

Daga nan suka yanke kayan da ke jikin keken guragun, inda a nan ne suka samu hodar Iblis din.

Da mutumin ya ga asirinsa ya tonu sai ya mike tsaye ya fara tafiya, inda mutane da ke wajen suka cika da mamaki.

An kama fakiti 11 na hodar Iblis mai nauyin kilo 13.25, kuma an kiyasin mutum 27,000 za su iya amfani da ita, kamar yadda ’yan sandan suka bayyana wa manema labarai.

Kimar hodar Iblis din za ta kai Yuro miliyan 1.4.

Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m