An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Akwai sansanonin gudun hijira da ke cikin yankunan masu haɗari kuma aka buƙaci su iya ƙaura nan take.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Benuwe (SEMA), ta gargaɗi mazauna yankin da ke da tazarar kilomita ɗaya da kogin Benuwe da su gaggauta yin ƙaura domin gujewa afkuwar ambaliyar ruwa.

Sakataren zartarwa na SEMA, Sir James Iorpuu, a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Makurdi a ranar Juma’a, ya ce hukumar ta samu sanarwa daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA), wanda ke nuni da cewa an samu ƙaruwar ruwa sosai.

Akwai yiwuwar samun ruwan sama na kwanaki biyar da zai haifar da mummunar ambaliyar ruwa a jihar.

Iorpuu ya lissafa yankunan da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar da suka haɗa da Udoma, Ugbokpo, Ugbokolo, Ukpiam, Otobi, Otukpo, Mbapa Makurdi, Gbajimba, Gogo da Abinsi.

Dangane da hakan ya jaddada buƙatar duk waɗanda abin ya shafa su bi umarnin wannan gargaɗin “domin yana da kyau a gare su kiyaye umarnin da tabbacin cewa ofishin hukumar tare da goyon bayan Gwamna Hyacinth Alia ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an samar wa ‘yan ƙasa kariya daga aukuwar iftila’i.”

Shugaban na SEMA ya ce sansanonin gudun hijira da aka keɓe su ma lamarin ana fargabar zai shafe su, inda aka buƙaci waɗanda ke yankunan da ke da haɗarin da su iya ƙaura nan take.

Ya ce mazauna Makurdi a Kanshio, Logo 1 da 2, Achussa, Judges Ƙuarters, kusa da Hotel Lucia da waɗanda ke zaune a kusa da BSU su koma Babbar Kasuwar Makurdi da ke kan titin George Akume.

Yayin da mazauna Kucha Utebe, Brewery, Gyado Villa, Mu da Wurukum za su koma makarantar firamare da ke Wurukum wadda aka fi sani da “Suswam Thank You.”

Ya kuma shawarci mazauna garuruwan RiceMill, Agboughu, Tionsha da Wadata da su koma makarantar firamare ta NKST da ke Wadata yayin da waɗanda ke bankin Arewa su koma makarantar firamare ta Katolika ta Saint Mary.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano