An bude asibitin Garun Kurama
An yi bikin bude asibitin da gwamnatin Jihar Kaduna ta gina a Garun Kurama da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. Da yake jawabi a lokacin karbar asibitin daga dan kwangilar da ya yi aikin Shugaban riko na karamar Hukumar Lere, Alhaji Adamu Sule ya gode wa gwamnatin jihar da dan majalisar da ke […]
An yi bikin bude asibitin da gwamnatin Jihar Kaduna ta gina a Garun Kurama da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a lokacin karbar asibitin daga dan kwangilar da ya yi aikin Shugaban riko na karamar Hukumar Lere, Alhaji Adamu Sule ya gode wa gwamnatin jihar da dan majalisar da ke wakiltar yankin kan gina asibitin, ya ce asibitin babban ci gaba ne ga al’ummar yankin. Ya yi kira ga al’ummar garin su kula da asibitin kuma su yi amfani da shi yadda ya kamata.
A jawabin shugaban sashin kiwon lafiya na karamar hukumar Alhaji Muhammad Sa’adu Kagarko ya yaba wa al’ummar Garun Kurama kan yadda suke ba ma’aikatan sashin hadin kai, inda ya yi kira gare su kan su kara kokari game da goyon baya da hadin kan da suke bayarwa kan harkokin kiwon lafiya.
Sakataren Hakimin Garun Kurama Mista Mala’ika Sadau ya mika godayar al’ummar garin ga Gwamnan Jihar Kaduna kan gina musu asibitin.
kan wannan asibiti da aka gina masu. Ya bada tabbacin cewa zasu yi
amfani da wannan asibiti kamar yadda ya kamata.