An bude cibiyar horar da akantoci a Gombe

kungiyar Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta yaye kwararrun akantoci 548 a cikin shekaru takwas daga Arewacin Najeriya. Malam Abbas Waziri, Babban-Daraktan tsare-tsare na Hukumar NNDC, shi ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata a Gombe a lokacin bikin bude cibiyar karatun ilimin kididdiga.A cewarsa, kwararrun akantocin 548 da aka yaye, an yi haka […]

An bude cibiyar horar da akantoci a Gombe
An bude cibiyar horar da akantoci a Gombe

kungiyar Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta yaye kwararrun akantoci 548 a cikin shekaru takwas daga Arewacin Najeriya.

Malam Abbas Waziri, Babban-Daraktan tsare-tsare na Hukumar NNDC, shi ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata a Gombe a lokacin bikin bude cibiyar karatun ilimin kididdiga.
A cewarsa, kwararrun akantocin 548 da aka yaye, an yi haka ne a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015 a cibiyoyin koyar da akantoci uku da ke Kano da Kaduna da Ilorin. Ya ce Jihar Gombe ce jiha ta hudu da aka bude irin wannan cibiya. Ya kuma bayyana gamsuwarsa da cewa yana sa ran cewa jihar ta bi sahun sauran jihohin nan uku wajen samar da kwararrun akantoci a wannan sabuwar cibiya da aka bude.
Waziri, ya kara da cewa wannan cibiyar, an kafa ta ne domin ganin an inganta da samar da matasan da za su zama kwararrun akantoci daga Arewacin Najeriya, musammam ma daga Jihar Gombe.
Da yake rantsar da shugabannin da za su shugabanci wannan makarantar, shugaban kungiyar Akantocin ta kasa, Otumba Samuel Deru, cewa ya yi cibiyar tana da rassa guda 53 a kasashen duniya, irinsu Amurka da Kanada da Ingila da Kamaru da nan gida Najeriya.
Ya ce sun kaddamar da bude wannan cibiyar ce a Jihar Gombe, don inganta darajar kwas din aikin akawu.
“NNDC ta sanya hannu a wata yarjejeniya da wannan cibiya ta mu a shekarar 2007 domin ganin an samu yawaitar kwararrun akantoci ne a yankin arewacin kasar nan,” inji shi.
A jawabinsa, Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan dankwambo, jinjina wa cibiyar koyar da kwararrun akantocin ya yi da cewa ta yi kokari ta samar da kayayyakin jarrabawa a cibiyar da kuma inda zai zama ofis.
Ya ce Gwamnatin Gombe za ta ba da dukkan wani irin tallafi da ake neman domin ganin an cin ma buri wajen yaye kwararrun akantoci a wannan cibiyar.
“Adadin yawan kwararrun akantoci da ake da su a wannan shiyya ta kasar nan ya yi kadan amma za mu ba da gudumawa wajen ganin an horar da wasu,” inji dankwambo.
Shi kuwa da yake jawabin amincewa da nada shi shugaban wannan cibiya na Jihar Gombe, Mista Kadiri Sajius alkawari ya yi na cewa za su yi aiki tukuru, ba za su bai wa jama’a kunya ba.