An bude cibiyar warware matsalolin masu mu’amala da kayan Samsung a Abuja

Shugaban Kamfanin na’urorin lantarki da wayoyin hannu na Samsung a Afirka ta Yamma, Mista Brobo Kim,  ya jagoranci bude cibiyar warware matsalolin masu mu’amala da kayan kamfani a Abuja.Mista Brobo ya yi bayani a lokacin bude ofishin kan fasahar kere-keren na’urori da kamfanin ke da shi, musamman a harkar sadarwa. Sannan ya bayyana yadda kamfanin […]

An bude cibiyar warware matsalolin masu mu’amala da kayan Samsung a Abuja

????????????????????????????????????

Shugaban Kamfanin na’urorin lantarki da wayoyin hannu na Samsung a Afirka ta Yamma, Mista Brobo Kim,  ya jagoranci bude cibiyar warware matsalolin masu mu’amala da kayan kamfani a Abuja.
Mista Brobo ya yi bayani a lokacin bude ofishin kan fasahar kere-keren na’urori da kamfanin ke da shi, musamman a harkar sadarwa. Sannan ya bayyana yadda kamfanin Samsung din ya bullo da dabarar shawo kan asarar masu mu’amala da kayansa, musamman wayoyin hannu, wadanda aka ba su wa’adin shekara biyu don yi wa mutum gyara, ko sake masa wayar da ya yi asara.
Wannan biki na bude wannan cibiya don inganta hulda da abokan cinikin kamfanin Samsung, ya samu halartar Shamm T. Kolo daga Hukumar Kare masu Sayen kayayyaki a Najeriya (CPC), wanda ya wakilci shugabar hukumar, Misis Modupe Atoki; da daraktan ayyukan kamfanin a Afirka ta Yamma, Raymond Olatokun.
Mista Brobo Kim ya bayyana cewa, akwai tsare-tsaren kare masu sayen wayoyin hannu na kamfanin Samsung, musamman masu tsada da ake yi wa lakabi da ‘smartphones,’ sannan akwai gyare-gyaren na’urori da za a rika yi wa mutane har a cikin gidajensu. Uwa-uba ya bayyana cewa Kamfanin Samsung ya bude cibiyoyin horar da masu gyaran na’urori a Jihohin Legas da Ekiti da Babban Birnin Tarayya Abuja. Ya kuma karkare bayanansa, ta hanyar bijiro da maganar shirin kare mutane daga asara, wanda aka yi wa lakabi da ‘ADH,’ wato sake wa mutum kayan da ya saya, matukar ba su kai shekara biyu a hannunsa yana amfani da su ba; ko kuma idan ya ga an fito da sabon kaya ya kawo nasa a karyar da shi, a rage masa kudin sabon, ya biya, ya dauka.
Shi kuwa jami’in Hukumar Kare Muradun Masu Sayen Kayayyaki a Najeriya (CPC), Injiniya Kolo, gargadin kamfanin ya yi kan lallai ya kyautata mu’amala da abokan huldarsa, ya kuma tabbatar da gaskiyar dilallan da yake hulda da su a fadin Najeriya. Domin a cewarsa, idan aka kawo musu kara kan rashin inganci kayan Samsung, to dole kamfanin ya dauki asara, amma idan suka tantance dilallalansu da wakilansu a fadin Najeriya, to za su shawo kan asarar a tsakaninsu da abokan ciniki. “A yi matukar kokari don kyautata wa abokan hulda. Domin mai sayen kayanka sarki ne, wajibi ne a kyautata masa ta yadda ciniki zai dore,” inji shi.
A nasa jawabin,Mista Raymond Olatukun , daraktan ayyuka a Afirka ta Yamma na Kamfanin Samsung ya tabbatar da cewa, kamfaninsa na matukar kokari wajen kyautata wa abokan huldarsa. “Muna matukar kokarin fadakarwa da wayar da kan masu hulda da kayayyakin da kamfaninmu ke kerawa,” inji shi.
Shi ma Injiniya Ahmad Magdy, babban darakta a sashen kula da gyaran na’urorin da kamfanin ke kerawa, ya bayyana manufar kamfaninsu ta kyautata wa masu sayen kayansu. Sannan ya yi godiya ga ’yan Najeriya da ke sayen kayansu. “Muna matukar godiya ga ’yan Najeriyar da ke sayen kayayyakinmu. Za mu tabbatar da cewa abin da kuka saya, ya yi daidai kimar kudin da kuka kashe don biyan bukatunku,” inji shi.
Jami’in shirya bikin, Mista Olusegun MacMedal, na kamfanin tallata haja na Upticomm, ya mika godiyarsa ga daukacin wadanda suka halarci wannan biki, tare da fatan za su ci gaba da hulda da Kamfanin Samsung, musamman wakilan kafafen yada labarai.