An bude gidan kukan huce takaici a India

An bude wani zaure a kasar Indiya inda za a rika zama domin jin labaran juna tare da yin kuka don huce takaici. Yayin da damuwa da takaici da kuncin rayuwa suka yi wa mutane yawa, su wadannan jama’ar sun dukufa ne domin samar wa jama’a mafita ta hanyar samar da wannan gida da jama’a […]

An bude gidan kukan huce takaici a India

An bude wani zaure a kasar Indiya inda za a rika zama domin jin labaran juna tare da yin kuka don huce takaici.

Yayin da damuwa da takaici da kuncin rayuwa suka yi wa mutane yawa, su wadannan jama’ar sun dukufa ne domin samar wa jama’a mafita ta hanyar samar da wannan gida da jama’a ke taruwa suna yin kukan huce haushi a bainar jama’a, domin samun saukin takaicin da ke damunsu.

A wani faifan bidiyo da kafar labarai ta BBC ta wallafa, an nuna mutane da dama suna ta sharar kuka a cikin wani zauren taro.

Wadannan mutane suna haduwa ne a wuri daya domin su yi kukan takaicin abin da ya dame su. Ana gudanar da taron ne a cikin zauren duk wata a Jihar Surat ta kasar Indiya. Wadanda suka assasa zauren sun ce sun assa shi ne domin suna da yakinin cewa kuka yana magance damuwa kuma yana taimaka wa lafiyar kwakwalwa.

Domin taimaka wa hawaye ya zubo, kowa yana tashi ne ya amayar da labarin matsalolin rayuwa da ya shiga, ko kuma su saurari kida mai taba zuciya domin kakalo kuka. 

Wani mai suna Jeeban Bhai wanda ya halarci zauren, ya ce yana jin dadi tare da samun saukin rayuwa idan ya ziyarci zauren “Ina jin dadi bayan mun gama wannan zama da muke yi. Ina ji tamkar an yaye min damuwa,” kamar yadda ya fada a faifan bidiyon. Ita ma wata budurwa mai suna Tanuja Shah da take halartar zaman ta ce takan huce takaicin da ke damunta matukar ta zo gidan domin wasu abubuwan suna boye wa iyayensu ne, “Muna boye wa iyayenmu wasu abubuwa da dama, sai kuma mu yi ta fama da damuwa daga baya. Ina fama da matsaloli da dama, amma zuwa wannan zaure yana taimaka min wajen rage damuwa,” kamar yadda ita ma ta sanar a faifan na bidiyo.

Mai shirya wannan zaure na kukan huce takaici, Kamlesh Masalawala ya ce suna shirya wannan zama ne domin su ba mutane dama su yi kuka su zubar da hawaye domin huce takaicin da ke damunsu na rayuwa. “Mun kirkiri wannan zaure ne domin taimaka wa mutane su samu abokan kuka. Kuma wannan waje yana taimaka musu domin su fitar da abin da ke damunsu cikin sauki. Shi ya sa ma muka sanya wa zauren suna ko taken: Daga hawaye zuwa shewa,” inji shi.

Amma shin da gaske ne zubar da hawaye yayin kuka yana ragewa ko magance bakin ciki da damuwa a zahiri?  A wani bincike da aka yi, ya nuna cewa kuka yana saukaka damuwar da mutum yake samun kansa a ciki. Amma sai dai akwai bukatar a tabbatar da wannan binciken ta hanyar zurfafa bincike a kan haka.