An bude gidauniyar kula da masu cutar kansa a Kano

Cibiyar wayar da kai da taimakon masu cutar kansa ta SALSUN da hadin gwiwar Cibiyar CHR mai kula da kuma bincike lafiya al’umma sun kafa gidauniyar tallafa wa matalauta masu fama da cutar kansa. A jawabinsa na Ranar Kansa ta Duniya ta 2021, Jami’in Shirin CHR, Malam Suleiman Umar Jalo ya ce an kafa gidauniyar […]

An bude gidauniyar kula da masu cutar kansa a Kano

Wata mara lafiya a gadon asibiti. (Tsohuwa ajiya).

Cibiyar wayar da kai da taimakon masu cutar kansa ta SALSUN da hadin gwiwar Cibiyar CHR mai kula da kuma bincike lafiya al’umma sun kafa gidauniyar tallafa wa matalauta masu fama da cutar kansa.

A jawabinsa na Ranar Kansa ta Duniya ta 2021, Jami’in Shirin CHR, Malam Suleiman Umar Jalo ya ce an kafa gidauniyar hadin gwiwar ce domin wayar da kai da kuma tattaro masu ruwa da tsaki don jinyar masu cutar.

Sannna ya ce an bude asusun banki da daidaikun mutane ko kamfanoni da hukumomi za su iya bayar da gudunmuwa don kula da masu cutar.

A nata bangaren, Shugabar SALSUN, Hajiya Hauwa Kakudi ta ce taken Rayar Cutar Kansa ta bana, ‘Ni ne kuma zan iya’ “ya nuna duk abin da muka yi na da tasiri ga mutanen da ke tare da mu.”

Ta ce an gano cewa karancin kayan aiki da tsadar magangani a wannan lokaci da ake fama da karancin kudi sun kawo cikas ga ba da kulawa da masu fama da cutar kansa a Najeriya ke bukata.

“Yawancin masu cutar kansa ba sa iya biyan kudin asibiti, wasu kuma cutar tasu ta yi tsanani da ke bukatar kulawa sosai amma ake samun jinkiri saboda rashin isassun kudade; su ne mutanen da gidauniyar ke da nufin taimaka wa,” inji ta.