An bude kasuwar zamani a Maradi

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Jamhuriyar Nijar tare da rakiyar wasu jami’an gwamnati suka isa Jihar Maradi domin bikin bude sabuwar kasuwar zamani da aka gina a jihar. An gina kasuwar ne tare da taimakon tallafin kasafin kudin kasar da Bankin Duniya da kuma da’irar birnin Maradi. Kasuwar na dauke da rumfuna guda 19,761. Shugaban […]

An bude kasuwar zamani a Maradi
An bude kasuwar zamani a Maradi

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Jamhuriyar Nijar tare da rakiyar wasu jami’an gwamnati suka isa Jihar Maradi domin bikin bude sabuwar kasuwar zamani da aka gina a jihar.

An gina kasuwar ne tare da taimakon tallafin kasafin kudin kasar da Bankin Duniya da kuma da’irar birnin Maradi. Kasuwar na dauke da rumfuna guda 19,761. Shugaban sabuwar kasuwar Lawali Leje a jajibirin bikin bude kasuwar, ya yi kira ga al’ummar Maradi da su fito kwansu da kwarkwatarsu don nuna jin dadi da godiya ga shugaba Mahammdu Issufu bisa wannan Jan aikin ci gaba a wannan jiha ta su da ya yi.
Ana nashi bangaren daya daga cikin shugabannin jam’iyya mai mulki Alhaji Zubeiru Lawali ya nuna jin dadinsa da godiya bisa cika alkawarin da shugaban ya yi tun a yakin neman zabe kuma ya cika. Da yake tsokaci wani dan jam’iyyar adawa ya koka game da yadda jami’an tsaro ke tursasawa al’umma a duk lokacin da shugaban kasar ya kawo ziyara jihar.Wannan ne dai karo na hudu da shugaban yake kawo ziyarar aiki jihar tun hawa kan kujerar mulki a watan Afrilun shekarar 2011.