An bude Makarantar Islamiyya ta zamani a Edo

An bude Makarantar Islamiyya ta zamani ta farko mai kunshe da bangaren boko a barikin soja na Bataliya ta 4 da ke Benin babban birnin Jihar Edo. Makarantar za ta rika karantar da darussan addinin Musulunci da na zamani musamman lura da yadda ake samun kalubale a makarantun allo a Arewa. Da yake yi wa […]

An bude Makarantar Islamiyya ta zamani a Edo
An bude Makarantar Islamiyya ta zamani a Edo

An bude Makarantar Islamiyya ta zamani ta farko mai kunshe da bangaren boko a barikin soja na Bataliya ta 4 da ke Benin babban birnin Jihar Edo.

Makarantar za ta rika karantar da darussan addinin Musulunci da na zamani musamman lura da yadda ake samun kalubale a makarantun allo a Arewa.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani game da makasudun gina makarantar, Babban Limamin Masallacin Barikin Bataliya ta Hudu, Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad ya ce “Abin da ya jawo hankalina na kafa makarantar shi ne ganin cewa akwai karancin irinsu a nan Jihar Edo, musamman birnin Benin, kodayake akwai guda uku da muka samu a kasa, amma suna da nisa sosai daga inda  muke, kuma game da kudin makaranta za ka iya cewa namu da sauki sosai. Kuma mun mayar da hankali ne wajen boko da Islamiyya, wanda bayan an tashi boko aka yi Sallar Azahar sai a shiga na addini zalla har zuwa Sallar La’asar.”

Manjo Kabiru Sa’ad ya ce, “Lura da yawan Musulmi a wannan wuri, amma babu irin wadannan makaratu na horar da ’ya’yan Musulmi da ba su tarbiyyar da ta dace irin ta Musulunci, ya sa muka kafa makarantar.”

Ganin babu irin wannan makaranta a kusa, ya sa yake bayar da tabbaci ga iyaye musamman farar hula da ke son kawo ’ya’yansu makarantar su kawo domin baya ga samun ilimi  “Ga kuma tsaro babu wanda zai yi fargaba yayin da ’ya’yansa suka fita zuwa makarantar karatu, zuwansu da komawarsu gida,” inji shi.

Babban Limamin ya kara da cewa kowa ya yi kokarinsa daidai gwargwado musamman bayan da aka kammala aikin domin sun bukaci kujeru da sauran kayan karatu an kuma samu daga al’ummar Annabi.

Manjo Yakubu Sa’ad ya ce “A gaskiya akwai bukata sosai  Musulmi su ci gaba da kula da ’ya’yansu, a rage sakaci. Musulmi sai dai su rika tura ’ya’yansu su je sauran makarantu da babu ruwansu da addini, wanda ya jawo sai ka ga yaro ko yarinya Musulmi amma babu alamun  Musulunci tare da su. Ya kamata a bai wa wannan yanki kula ta musamman ganin halin ci baya da suke  ciki.”