An bude Makarantar Tsangaya da Namadi Sambo ya gina a Bauchi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka bude makarantar Tsangaya da Mataimakin Shugaban kasa Muhammed Namadi Sambo ya gina wa Sheikh dahiru Usman Bauchi a kusa da kauyen Kangyare a kan hanyar zuwa Gombe da aka kashe miliyoyin Naira wajen gina ta, domin koyar da yara karatun addini da na zamani. Da yake tofa […]

An bude Makarantar Tsangaya da Namadi Sambo ya gina a Bauchi
An bude Makarantar Tsangaya da Namadi Sambo ya gina a Bauchi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka bude makarantar Tsangaya da Mataimakin Shugaban kasa Muhammed Namadi Sambo ya gina wa Sheikh dahiru Usman Bauchi a kusa da kauyen Kangyare a kan hanyar zuwa Gombe da aka kashe miliyoyin Naira wajen gina ta, domin koyar da yara karatun addini da na zamani.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo wanda Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi Alhaji Ibrahim Muhammed Aminu ya wakilta, ya ce Mataimakin Shugaban kasa Namadi ya gina makarantar ne domin ba da tasa gudunmawa wajen ciyar da addinin Musulunci gaba.
A jawabin Sheikh dahiru Usman Bauchi ya nuna godiyarsa ga Alhaji Namadi Sambo bisa yadda ya cika alkawarin da ya dauka.
Da yake zantawa da Aminiya a wajen taron, Daraktan Makarantun Tsangaya na Jihar Bauchi, Sayyadi Aliyu Sheikh dahiru Bauchi, ya ce an zuba dukkan kayayyakin da suka kamata kamar kwamfuta da sauran kayayyakin karatu na zamani a makarantar.
Ya roki gwamnatin jihar da ta ba da kulawa ta musamman domin ci gaban makarantar, inda ya ce za su ci gaba da yin addu’o’i na musamman ga Mataimakin Shugaban kasa Namadi sambo inda ya ce mutum ne da yake da kishin addinin Musulunci.
Khalifa Sheikh Ahmad Tijjani Ibn Sheikh Ibrahim Nyass ne ya jagoranci bikin bude makarantar tare da Jakadan kasar Senegal a Najeriya da sauran manyan baki da suka fito daga sassa daban-daban na Nahiyar Afirka.