An bude makarantun Bayelsa bayan hutun dole
Gwamnatin jihar Bayelsa ta bayar da sanarwar bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar. Inda zasu fara karatu a yau 5 ga watan Nuwamba 2018, bayan rufe makarantun na watanni sanadiyyar ambaliyar ruwa. Kwamishinan ilimi na jihar Bayelsa Jonathan Obuebite ne, ya sanar da hakan inda ya umarci shugabanni makarantun sakandare da malamai […]
Gwamnatin jihar Bayelsa ta bayar da sanarwar bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar. Inda zasu fara karatu a yau 5 ga watan Nuwamba 2018, bayan rufe makarantun na watanni sanadiyyar ambaliyar ruwa.
Kwamishinan ilimi na jihar Bayelsa Jonathan Obuebite ne, ya sanar da hakan inda ya umarci shugabanni makarantun sakandare da malamai da masu makarantu da dalibai da iyaye da su dawo su ci gaba zangon karatu na 2018/2019