An bude manyan ayyukan amfanin jama’a a Ibadan
Ranar Talata ne shugabannin jam’iyar ACN na kasa da gwamnoni da sarakuna da wasu manyan mutane suka halarci bukukuwan da Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yi wajen bude wasu muhimman ayyukan amfanin jama’a. Ayyukan sun hada da gadar sama a Mokola da sabon garejin tsayuwar motoci na zamani da ke Podo da sabuwar […]

Ranar Talata ne shugabannin jam’iyar ACN na kasa da gwamnoni da sarakuna da wasu manyan mutane suka halarci bukukuwan da Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yi wajen bude wasu muhimman ayyukan amfanin jama’a. Ayyukan sun hada da gadar sama a Mokola da sabon garejin tsayuwar motoci na zamani da ke Podo da sabuwar kasuwa da ke ‘scount camp challenge’, dukansu a Ibadan.
A watan Disamban shekarar 2011 ne aka bayar da kwangilar gina gadar domin magance cunkoson abubuwan hawa, wand ya samu suka daga ’yan hamayya kafin a kammala shi. ’Yan hamayyar, wadanda suna tare da tsofaffin gwamnoni Rashid Ladoja da Adebayo Alao Akala da yanzu suka kulla kawance domin tunkude ACN daga mukin jihar a zaben shekarar 2015.
Sai dai jagoran ACN, tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya shaida wa dimbin mahalarta bikin cewa, kawancen ba zai yi tasiri ba domin al’ummar Jihar Oyo, sun dawo daga rakiyarsu, musamman ma ayyukan da Gwamna Ajimobi ya shimfida a cikin shekaru 2, sun kasa yin irinsu a shekaru 8 da suka yi suna mulki a jihar.
Gwamna Abiola Ajimobi, a jawabinsa ya ce kammala ayyukan, musamman wannan gadar sama, mafarkinsa ne ya tabbata, domin “Lokacin da muka fara, ’yan hamayya sun yi ta kulle-kullen kutunguila da makirci domin ganin bamu kai ga nasara ba, amma, Allah ya fi su. Yanzu muka fara aikin kyautata rayuwar jama’a. Na gaba ya yi gaba. Na baya sai tsintar hula.” inji shi.
Bikin ya samu halartar shugaban jam’iyar ACN na kasa Cif Bisi Akande da gwamnonin jihohin Osun Rauf Aregbesola da Ogun Ibikunle Amosun da Imo Rochas Okorocha da mataimakiyar gwamnan Jihar Legas Uwargida Adejoke Orelope-Adefulire, wadda ta wakilci Gwamna Babatunde Fashola da jagoran musulmi na kasar yarbawa Alhaji Abdul-Azeez Arisekola Alao. Mai martaba Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi shi ne ya jagoranci sarakuna a wajen bikin.
Sai dai ’yan kasuwa a kananan hukumomin da aka gudanar da bukukuwan a cikin huruminsu ba su ji da dadi ba saboda an hana su baje kolinsu a lokacin bikin.