An bude ofishi tare da kaddamar da shugabanin Jam’iyyar APC a Gombe
A makon jiya ne aka bude sakatariyar Jam’iyyar APC na Jihar Gombe tare da kaddamar da shugabanin jam’iyyar na rikon kwarya da Alhaji Umar Duhu, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Gabas ya kaddamar.Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da shugabannin rikon, Alhaji Umar Duhu, ya shawarce su kan su rungumi kowa da […]

A makon jiya ne aka bude sakatariyar Jam’iyyar APC na Jihar Gombe tare da kaddamar da shugabanin jam’iyyar na rikon kwarya da Alhaji Umar Duhu, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Gabas ya kaddamar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da shugabannin rikon, Alhaji Umar Duhu, ya shawarce su kan su rungumi kowa da kowa a tafi tare wajen yi wa jama’a rajistar kasancewa ’yan jam’iyyar.
Ya ce ba su da niyyar nuna wariya ga kowa, nema suke su dinke duk wata baraka da ke tsakanin ’ya’yanta tunda APC sabuwar jam’iyya ce ba sa kaunar a ce wata rigima ta taso.
Alhaji Umar, ya musanta zargin da tsohon dan takarar Gwamna na rusasshiyyar Jam’iyyar CPC a Jihar Gombe Alhaji Abubakar Aliyu cewa ba sa tare da shugabannin da aka kaddamar saboda ba ’yan jam’iyyar adawa ba ne, inda ya ce tunda Abubakar Aliyu ya yi takara a CPC bai ci ba, ya yi wa jam’iyyar butulci kuma sun yi ta nemansa ya dawo a tafi tare ya rika yi musu was an-buya.
“Kuma muna zargin shugabanin Jam’iyyar PDP ne suke amfani da shi wajen neman kawo wa APC cikas don har maganar da muke yi da ku bai yarda mun zauna da shi don a tafi tare ba,” inji shi.