An bude ofishin kamfen din Buhari a Jihar Osun
Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa ya shiga Jihar Osun, inda ya yi kicibis da ’yan takarar Gwamna da magoya bayansu daga jam’iyyu daban-daban da suke yawon isar da kansu ga jama’a don su zabe su a matsayin Gwamna a zaben da za a yi gobe Asabar a jihar. […]

Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa ya shiga Jihar Osun, inda ya yi kicibis da ’yan takarar Gwamna da magoya bayansu daga jam’iyyu daban-daban da suke yawon isar da kansu ga jama’a don su zabe su a matsayin Gwamna a zaben da za a yi gobe Asabar a jihar.
A daidai lokacin da kungiyar a karkashin jagorancin Alhaji danladi Pasali ke kokarin bude sabon ofishin yakin zaben Shugaba Buhari ne aka hango tawagar magoya bayan ’yan takarar Gwamna a jam’iyyun PDP da ADC suna wucewa a kan babbar hanyar Gbongan, inda suka rika hararar juna da wakokin habaici. An girke ’yan sandan kwantar da tarzoma a wurin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Da yake yi wa Aminiya bayani jim kadan bayan bude ofishin na Jihar Osun, Alhaji danladi Pasali ya ce kungiyar ta fito ne domin ziyarar jihohi 36 na kasar nan da za a bude irin wannan ofishi, wanda za a tanadar masa da na’urorin zamani a ciki domin samun sauki ga jama’a masu bukatar sanin bayanan irin muhimman ayyukan da Shugaba Buhari ya yi a cikin shekara 3 a sassan kasar nan. Ya ce, irin na’urorin da za a girke a cikin ofisoshin, za su taimaka wajen fito da bayanai dalla-dalla kan irin ayyukan Shugaba Buhari, sabanin bayanan da masu hamayya suke yi cewa babu wani abin a zo a gani da wannan gwamnati ta yi.
Da yake amsa wata tambaya Alhaji Pasali cewa ya yi, “Dokar Najeriya da dokar Jam’iyyar APC ba su haramta tara kudi domin sayen fom ga duk mutumin da magoya bayansa suka yi masa shaidar amana da adalci da kishin kasa da suke so ya tsaya a takarar wani mukami ba. Saboda haka ban ga dalilin da masu hamayya suke sukar wannan lamari da jama’ar kasa da kansu suka tara kudin sayan fom ga Shugaba Buhari ba tare da an nema daga gare su ba.”
Shugabannin wannan kungiya na jihohi 6 a Kudu maso Yamma tare da dimbin magoya baya ne suka halarci bikin bude ofishin. Akwai da yawa daga cikin mahalarta taron da suka yi wasu tambayoyi musamman a kan matsalolin da suka fuskanta wajen sanin wuraren karbar katin zabe, inda wakilan kungiyar suka ba su amsa da bayanai masu gamsarwa.